Yara masa cutar tamowa sun ƙaru da 51% a Najeriya —Likitoci

Shugaban Ƙungiyar MSF, Dokta Christos Christou, ya ce ƙananan yara 52,725 masu fama da cutar tamowa ne ƙungiyar ta kwantar a Najeriya a cikin watanni takwas na farkon shekarar 2024

Yara masa cutar tamowa sun ƙaru da 51% a Najeriya —Likitoci

Ƙungiyar Likitoci ta Duniya (MSF) ta bayyana cewa yawan yara masu fama da cutar tamowa a Najeriya ya karu da kashi 51% a watanni takwas na farkon shekarar 2024 a Najeriya.

Shugaban Ƙungiyar MSF, Dokta Christos Christou, ya sanar da cewa ƙananan yara 52,725 masu fama da cutar tamowa ne ƙungiyar ta kwantar a Najeriya a tsawon lokacin.

Tamowa ita ce cutar matsananciyar yunwa da rashin ingantaccen abinci mai gina jiki, wadda kuma take barazana ga rayuwar ƙananan yara.

Dokta Christos Christou ya sanar a Abuja cewa adadin yaran da suka kamu da tamowa a Najeriya ya ƙara ƙaruwa, idan aka kwatanta alƙaluman shekarar 2022.

Ya ce, “babban musabbabin shi ne cututtukan da za a iya kare aukuwarsu Najeriya irin su ƙyanda, wadda ke cikin cututtukan da suke yawan yin ajalin ƙananan yara.

“Daga watan Janairu zuwa Agustan wannan shekara kaɗai mun duba lafiyar yara 12,500 masu fama da cutar kyanda, wanda ya kusa ninka adadin da aka samu a bara.

“Ɓullar cututtuka masu yaɗuwa na ƙara barazanar mace-macen yara ’yan ƙasa da shekaru biyar.

“Yaran da ba a yi musu alluran rigakafin cututtukan ba sun fi shiga haɗari; kuma cututtukan suna ƙara kawo barazanar tamowa.”

Ya bayyana cewa ya shaida yadda ambaliyar Maiduguri ta girgiza al’ummar duniya, duk da cewa yankin Arewacin Najeriya na fama da wasu ƙarin bala’o’i.

Matsalolin a cewarsa sun haɗa da tamowa da yawan ɓarkewar cututtuka da za a iya daƙile su da alluran rigakafi.

Sauran matsalolin su ne ƙarancin cibiyoyi da ma’aikatan kiwon lafiya.

A cewarsa, “waɗannan matsalolin ƙari ne a kan matsalar rashin tsaro.”

Ya ce bayan ambaliyar Maiduguri kungiyar ta kafa Cibiyar jinyar masu kwalara bayan ɓullar cutar.

“Wannan matsalar ta ɓullo ne a yayin da ake fama da tamowa.

“Wani abokin aikina likita da ake aiki da MSF a Najeriya tsawon shekaru takwas ya shaida min cewa a bana matsalar ta fi muni.

“Duk shekara ana kwantar da ɗimbin yara a sakamakon tamowa, amma a bana lokacinnd aka saba ganin raguwar matsalar ta yi, amman duk da haka adadin da tsananin cutar sai ƙaruwa suke yi.

“Yawancin mutanen kuma babu cibiyoyin kiwon lafiya a yankunan da suke ko kuma ba su da kuɗin zuwa asibiti, don haka suke zuwa wurin a makare,” in ji shi.

Mutum 10 sun mutu a wajen rabon tallafin abinci a Abuja

Tirela murƙushe ’yan sanda 3 har lahira

An ƙwace kwantainoni 54 mallakin Emefiele

Fulawa da dabbobin Fadar Shugaban Ƙasa za su ci N125m a 2025