Yara miliyan 10 ba sa zuwa makaranta a Najeriya – UNICEF
Yara miliyan goma da rabi ne ba su samun shiga makarantun firamare a Najeriya saboda da rashin galihu da karancin daukar dawainiyar karatunsu daga iyaye ko gwamnati.Jami’in kula da ilimin yara na Hukumar Yara ta Majalisar dinkin Duniya (UNICEF) Dokta danjuma Almustapha ne ya bayyana haka a wurin wani taron bita da hukumar ta shirya […]
Yara miliyan goma da rabi ne ba su samun shiga makarantun firamare a Najeriya saboda da rashin galihu da karancin daukar dawainiyar karatunsu daga iyaye ko gwamnati.
Jami’in kula da ilimin yara na Hukumar Yara ta Majalisar dinkin Duniya (UNICEF) Dokta danjuma Almustapha ne ya bayyana haka a wurin wani taron bita da hukumar ta shirya wa manema labarai domin su wayar da kan jama’a.
Ofishin UNICEF mai lura da jihohi 10 da ke Bauchi ne ya shirya bitar ga ’yan jaridar da suka fito daga jihohin shiyyar don tayar musu da tsimi wajen nemo rahotanni da bincike kan koma baya da ake samu wajen shigar yara makaranta.
Dokta danjuma Almustapha ya ce a Arewa akwai kimanin yara miliyan shida da rabi da ba su samu shiga makaranta ba, kuma Arewa maso Gabas ce a sahun gaba kan rashin zuwa makaranta.
Ya bukaci iyaye da gwamnati da shugabannin addini su hada hannu don samar da makarantu da horar da malaman da suka dace da gudanar da aikin ilimantar da yaran yankin.
Ya kira yi gwamnatocin Arewa su samar da kudi da tsari mai kyau don samar da wadatattun makarantu da malamai a yankunan karkara tare da sa ido don tabbatar da kudin da ake kashewa kan ilimi an yi aiki da shi a hanyar da ta dace.
Dokta Almustapha, ya ce ya kamata a samar da ingantaccen tsaro a Arewa domin kowa ya samu damar sauke nauyin da yake kansa, musamman a wannan lokaci da ake lalata makarantu da kashe dalibai da malamai.