‘Yara miliyan 16 ne aka haifa lokacin yaki’
Asusun Kula da Yara na Majalisar dinkin Duniya (UNICEF), ta ce yara miliyan 16 aka haifa a yankunan da ke fama da yaki cikin wannan shekara.A cewar Shugaban Hukumar UNICEF, Anthony Lake, a kowace dakika biyu ana haifar jariri a wurin da ake tsakiyar fadace-fadace kuma yara da yawa na girma a cikin matsanancin yanayi […]
Asusun Kula da Yara na Majalisar dinkin Duniya (UNICEF), ta ce yara miliyan 16 aka haifa a yankunan da ke fama da yaki cikin wannan shekara.
A cewar Shugaban Hukumar UNICEF, Anthony Lake, a kowace dakika biyu ana haifar jariri a wurin da ake tsakiyar fadace-fadace kuma yara da yawa na girma a cikin matsanancin yanayi na rayuwa, kama daga tashe-tashen hakula da bala’o’i da fatara da cututtuka da yunwa.
Wadannan alkaluma sun yi daidai da yaro daya a cikin yara takwas da ake haifa.
Hukumar ta yi gargadin cewa akwai yiwuwar wadannan yara su mutu kafin su cika shekara biyar, sannan wadanda suka rayu za su iya samun matsala a tunaninsu.