Yara miliyan daya ne ba su zuwa makaranta a Zamfara – SUBEB
Jihar Zamfara tana da yara sama da miliyan daya da ba su zuwa makaranta, lamarin da ya sa ta zamo ta daya a kasar nan wajen yawan yaran da ba su zuwa makaranta.Daraktan kananan Makarantun Sakandare na Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar (SUBEB), Alhaji Sani Mailafiya ne ya bayyana haka a Gusau, lokacin da yake […]

Jihar Zamfara tana da yara sama da miliyan daya da ba su zuwa makaranta, lamarin da ya sa ta zamo ta daya a kasar nan wajen yawan yaran da ba su zuwa makaranta.
Daraktan kananan Makarantun Sakandare na Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar (SUBEB), Alhaji Sani Mailafiya ne ya bayyana haka a Gusau, lokacin da yake magana a wurin taron tattaunawa kan yadda za a farfado da ilimi a jihar.
Alhaji Sani Mailafiya ya shaida wa masu ruwa da tsaki a wurin taron cewa sun tabbatar da yawan daliban da ke kowace makaranar firamare ta hannun kwamitin duba ilimi da sanya ido.
Da yake gabatar da takarda a wurin taron Shugaban karamar Hukumar kauran Namoda, Alhaji Lawalli Liman ya ce cikin kashi 70 cikin 100 na yara da suka isa shiga makarantar firamare kashi 50 ne kawai suke kammalawa su shige sakandare. “Kuma cikin masu karatu a manyan makarantun sakandare sakamakon da ke zuwa daga WAEC da NECO abin ya fi muni, saboda Zamfara tana zuwa kashin baya a jarrabawar WAEC da NECO, wanda hakan ke shafar takaita yawan daliban da suke zuwa manyan cibiyoyin ilimi daga jihar,” inji shi.
Liman ya yi bayanin cewa dalilai da dama ne suke tabbatar da ingancin ilimi ga dalibai da suka hada da samun kwararrun malamai, kuma wannan kwarewa ta shafi yanayin zurfin ilimi da ingancin albashi da kuma karfafa gwiwar malaman, kuma inganta wadannan zai haifar da kyakkyawan sakamako.