Yara uku sun rasu bayan kasa ta rufta musu a Kaduna

A makon jiya ne wadansu yara uku suka rasa rayukansu bayan kasa ta rufta musu a Unguwar Karshen Kwalta da ke Rigasa a Karamar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna. Lamarin wanda ya  faru da misalin karfe 3:30 na yamma ya jefa al’ummar unguwar cikin rudani. Aminiya ta samu labarin cewa biyu daga cikin yaran sun rasu […]

Yara uku sun rasu bayan kasa ta rufta musu a Kaduna
Yara uku sun rasu bayan kasa ta rufta musu a Kaduna

A makon jiya ne wadansu yara uku suka rasa rayukansu bayan kasa ta rufta musu a Unguwar Karshen Kwalta da ke Rigasa a Karamar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna.

Lamarin wanda ya  faru da misalin karfe 3:30 na yamma ya jefa al’ummar unguwar cikin rudani.

Aminiya ta samu labarin cewa biyu daga cikin yaran sun rasu nan take bayan kokarin da jama’a suka yi na fito da su ya ci tura.

Shi kuma daya daga cikinsu ya rasu ne sa’o’i kadan bayan an ceto shi daga cikin ramin.

Yara biyar abin ya shafa kuma dukkansu shekaransu sun fara ne daga 12 zuwa 16.

A yanzu haka biyu daga cikinsu suna kwance a wani asibiti inda suke jinya.

Babban Limamin Masallacin Juma’a na Karshen Kwalta, Malam Jamilu wanda shi ne ya sallaci gawarwakin yaran ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Ya ce yaran sun je hakar karfe ne a wajen da gwamnatin jihar ke yin wani gyaran gada a unguwar.

“An bayyana cewa sun je wajen ne domin hakar karfe a wajen da ake aikin gada. Suna cikin hakar ce kasa ta rufta musu. Daya daga cikin yaran mai suna Zahradin dan makwabcina ne,” inji shi.

Ya kara da cewa kwanansu ne ya kare domin an rika korarsu daga wajen amma sai suka koma.

“Akwai matar da ta ga lokacin da kasar ta rufta musu, sai ta yi kuwwa aka taru a wajen amma ba a iya ciro su ba, Allah Ya jikansu,” inji shi.

Wani mazaunin unguwar mai suna Ahmad ya ce da jama’a suka taro yaran na da sauran ransu, amma rashin kayan aikin da za a yi amfani da shi wajen ceto rayuwarsu ya sa suka rasu.

Tuni aka yi jana’izarsu kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.