Yaran Ali kwara sun bindige ’yan fashi a Kaduna
Shahararren mai kama barayin nan, Alhaji Ali kwara ya bayyana cewa mutanensa sun halaka wasu ’yan fashi uku tare kuma da raunata biyu a wani artabu da suka yi da ma’aikatansa a kan hanyarsu ta barin Birnin Gwari.A cewarsa, ’yan fashin da ke a cikin wata mota kirar Gulf daga Birnin Gwari suke kuma an […]

Shahararren mai kama barayin nan, Alhaji Ali kwara ya bayyana cewa mutanensa sun halaka wasu ’yan fashi uku tare kuma da raunata biyu a wani artabu da suka yi da ma’aikatansa a kan hanyarsu ta barin Birnin Gwari.
A cewarsa, ’yan fashin da ke a cikin wata mota kirar Gulf daga Birnin Gwari suke kuma an same su da bindigogi kirar AK-47 bakwai da kuma kirar dabul-barel daya sannan da harsasai sama da dubu daya a cikin motarsu.
kwara ya bayyana haka a yayin zantawarsa da manema labarai. Ya ce al’amarin ya auku ne a ranar Lahadin da ta wuce.
“Ma’aikatana ne tare da hadin gwiwar ’yan sanda na musamman da aka kafa domin su rika bi na zuwa kamo bata-gari ne suka yi artabu da su a kan hanyarsu ta barin Birnin Gwari zuwa Jos. Sannan sun yi nasarar bindige uku daga cikinsu, biyu kuma sun gudu da raunuka,” inji shi.
Ya kuma ce mafi yawancin ’yan fashin da ke addabar mutane a Birnin Gwari mutane ne da suka yi hijira daga jihohin Katsina da Zamfara zuwa Kaduna.
Haka kuma ya bayyana wani mai suna Shehu kwara da aka kama a kwanakin baya a matsayin sojan-gona yana cewa wai shi ne Ali kwara. “karya yake yi, tsohon mai laifi ne shi, sojan-gona yake min. Yana bi ne yana karbar kudade a hannun kauyawa ’yan Fulani da sunan wai ya kama su. A yanzu haka na samu bayanin ya fara biyan kudin da ya kwata a hannun mutane.” Inji shi.