Yaran da ba a yi wa rigakafi ba da ake dawo da su Najeriya daga waje barazana ne – Hafsat Yusuf

Shugabar Gidauniyar ’Mothers of the Earth International Foundation,’ Hajiya Hafsat Yusuf, ta koka kan yawan yaran ake tafiya Turai da su ba bisa ka’ida ba da ake dawowa da su Najeriya ba tare da an yi musu allurar rigakafi ba, inda ta bukaci hukumomi su dauki mataki a kai. Shugabar ta bayyana haka ne a […]

Yaran da ba a yi wa rigakafi ba da ake dawo da su Najeriya daga waje barazana ne – Hafsat Yusuf

Shugabar Gidauniyar ’Mothers of the Earth International Foundation,’ Hajiya Hafsat Yusuf, ta koka kan yawan yaran ake tafiya Turai da su ba bisa ka’ida ba da ake dawowa da su Najeriya ba tare da an yi musu allurar rigakafi ba, inda ta bukaci hukumomi su dauki mataki a kai.

Shugabar ta bayyana haka ne a lokacin da ta kawo ziyara hekdwatar Kamfanin Media Trust mai buga jaridun Daily Trust da Aminiya, inda ta ce, adadin yaran da ba a yi musu rigakafin ya kai wanda mahukunta za su sa baki lura da yadda gwamnati da sauran kungiyoyi na gida da na waje suka hada karfi da karfe wajen kawar da cututtukan da kan shafi jarirai da kananan yara da suka hada da shan inna da shakau da sauransu.

Gidauniyar ’Mothers of the Earth International Foundation kungiya ce mai zaman kanta da ke Abuja da take yaki da zuwa kasashen Turai ba bisa ka’ida ba da kuma aikin jinkai don rage talauci a tsakanin matan da suka rasa mazansu.

Hajiya Hafsat ta ce mafi yawan jarirai da kananan yaran da hukumomin kasashen Turai suka taso keyarsu zuwa Najeriya saboda shiga kasashensu ba bisa ka’ida ba suna dawowa ne ba tare da an yi masu allurar rigakafi na wata shida da suke kare su daga cututtuka 14 da ake yi a nan Najeriya. Don haka ta bukaci iyayen wadannan yara cewa da zarar sun dawo Najeriya wajibi ne su kai ’yan’yansu a yi musu allurar rigakafin a asibiti mafi kusa.

“Makasudin wannan ziyara tamu shi ne mu nemi hadin kan kamfanin jaridun Trust da Aminiya kan yakin da muke yi da hijira zuwa kasashen Turai ba bisa ka’ida ba. Muna so ku wayar da kan jama’a musamman ’yan Najeriya cewa, hijira abu ne mai kyau amma idan an bi ka’idojin da suka kamata. Amma yanzu matsalar da ta addabi Najeriya ita ce ta shiga Turai ta barauniyar hanya. Kuma ta wannan hanya ce ake yaudarar matasa a yi safararsu zuwa Turai da sunan za a samar musu aiki,” inji ta.

Ta ce “Mafi yawan lokuta akan sayar da su ne a matsayi bayi ko  a tilasta yin karuwanci. Kuma idan an kamo su an dawo da su nan Najeriya za a iske ’ya’yan da suka dawo da su ba a yi masu allurar rigakafi ba. Hakan na nufin za su iya yada cututtukan da aka riga aka kauwar da su a kasar nan.”

Da yake karbarsu a madadin Shugaba kuma Babban Editan  Kamfanin, Malam Mannir Dan’Ali, Mataimakin Manajan Edita, Malam Nasiru Imam, ya ce jaridun Daily Trust da Aminiya a shirye suke su hada kai da gidauniyar  don wayar da kan jama’a game da illolin zuwa ci-rani kashen waje ba bisa ka’ida ba.

Malam Nasir ya ce jaridun za yayata ayyukan jinkai da kungiyar ke yi a sansanonin ’yan gudun hijira a Najeriya.

Tun farko Kakakin gidauniyar, Mista Soji Bamidele ya mika godiya ga jaridun Trust da Aminiya bisa gudunmawar da suke bayarwa a fannin zaman lafiya da wayar da kan jama’a, inda ya nemi sauran kafafen watsa labarai su yi koyi da jaridun.