Yaran da suka gudu kan zargin kuntatawa sun koma hannun iyayensu
Yaran nan uku da Aminiya ta ba da labarin guduwarsu daga gidan mahaifinsu da ke garin Jiwa a yankin Birnin Tarayya, Abuja kan zargin kuntatawa, sun koma hannun iyayensu bayan mako shida da faruwar al’amarin. Fatima Auwal mai shekara 11 da kannenta Sa’adiyya mai shekara bakwai da Kabir mai shekara bioar, sun baro gidansu ne […]
Yaran nan uku da Aminiya ta ba da labarin guduwarsu daga gidan mahaifinsu da ke garin Jiwa a yankin Birnin Tarayya, Abuja kan zargin kuntatawa, sun koma hannun iyayensu bayan mako shida da faruwar al’amarin. Fatima Auwal mai shekara 11 da kannenta Sa’adiyya mai shekara bakwai da Kabir mai shekara bioar, sun baro gidansu ne kan zargin kuntata musu da suka ce matar mahifinsu na yi, kuma an gan su ne suna watangaririya a kusa da tashar motar Zuba a kan hanyarsu ta zuwa wajen mahaifiyarsu a kauyen Kasanga a karamar Hukumar Mariga ta Jihar Neja, inda suka shirya zuwa da kafa.
A zantawarsa da Aminiya a fadar Sarkin Zuba a ranar Asabar da ta gabata, mahaifin yaran Malam Muhammad Lawal wanda ya je fadar tare da mahaifiyarsu Malama A’isha Jibrin a ranar Juma’a da ta gabata, ya ce ya samu labarin gane yaran ne ta waya daga wurin wani abokinsa da ke garin Gwagwa, Abuja bayan sanya labarin a jaridar Aminiya ta ranar, a lokacin yana kasuwar Tegina da ke Jihar Neja, kuma nan take inji shi ya sanar da mahaifiyarsu wadda suka taho fadar tare. Ya ce batar yaran ya jawo masa damuwa matuka ciki har da kara nisantarsa da mahaifiyar yaran ta yi bayan ta baro gidansa kamar wata biyu ke nan a yanzu sakamakon sabani a tsakaninta da matarsa ta biyu, in ji shi.
Malam Auwal ya ce wasu a garinsu sun yi zargin cewa sayar da yaran ya yi don neman abin duniya. Kuma ya gode wa fadar Sarkin Zuba kan kula da yaran da kuma jaridar Aminiya wanda ya ce ta zamanto dalilin gano ’ya’yansa.
Mahaifiyar yaran, Malama A’isha Jibrin cewa ta yi batar yaran ta jefa rayuwarta cikin kunci, sai dai duk da hakan inji ta ba su yanke kauna ba, inda ta ce danginta da na mijinta sun ci gaba da sanya malamai suna addu’a a wurare daban-daban.
Sarkin Fadar Zuba, Malam Muhammad Murtala wanda ya wakilci Agoran Zuba Alhaji Muhammadu Bello Umar, kira ya yi ga ma’auratan su sasanta tsakaninsu, kuma su kyautata kula da ’ya’yansu.
Sarkin Fadar ya mika yaran ga Wakilin Jiwa Malam Ibrahim Muhammad wanda zai mika su ga Sarkin Jiwa Alhaji Idris Musa kafin mika su ga iyayensu.