Yarbanci na cikin harsunan da ake so don daukar ’yan sanda a Ingila
Mahukuntan ’yan sandan Birtaniya (British Metropolitan Police) sun bullo da wani tsari da tilas wanda ke son a dauke shi a aikin dan sanda ya iya wani harshe baya ga Ingilishi, inda harshen Yarbanci ya shiga sahun harsunan da ake so mutum ya isa kafin a dauke shi aiki.Hukumar ’yan sandan yankin Scotland Yard ta […]
Mahukuntan ’yan sandan Birtaniya (British Metropolitan Police) sun bullo da wani tsari da tilas wanda ke son a dauke shi a aikin dan sanda ya iya wani harshe baya ga Ingilishi, inda harshen Yarbanci ya shiga sahun harsunan da ake so mutum ya isa kafin a dauke shi aiki.
Hukumar ’yan sandan yankin Scotland Yard ta wajabta wa masu son shiga aikin dan sanda iya daya daga cikin harsuna 14 da ake amfani da su a sassan birnin Landan.
Jaridar Dailymail (Ingila) ta ruwaito cewa a wani bangare na gwajin wata daya da aka fara a ranar Talatar da ta gabata, wajibi ne sababbin dauka a aikin dan sanda su iya magana da Ingilishi da Yarbanci ko Larabci ko Hebrew ko Hindu ko Punjabi ko Italiyanci ko Jamusanci Turkanci ko yaren nutanen Girka ko na mutanen Spain ko na Poland ko na Portugal ko Sinhala (na mutanen Sri Lanka) ko kuma Bengali kafin a dauke su a aikin na dan sanda.
Wannan mataki dai ya sha suka daga wani tsohon dan sanda da kuma jama’ar gari a shafukan Twitter.
dan sandan birnin Landan mai ritaya Chris Hobbs ya rubuta cewa: “Na yi ta karantawa ina sake karanta bayanin. Ban gaskata abin da na gani ba. Mene ne makomar sauran bakake da kananan kabilu wadanda Ingilishi kawai suka iya?
Ya kara da cewa “Ba a jin wannan zai shafi daukar ’yan sanda samari da ’yan mata da suka fito daga al’ummar bakaken fata da suke da sha’awa.”
Bayan da Kwamishinan ’Yan sanda Bernard Hogan-Howe ya tsara burin ganin kashi 40 cikin 100 na daukacin ’yan sanda sun fito daga bakaken fata da sauran kabilu marasa rinjaye, kashi 18 cikin 100 ne kacal suka cika ka’idar dauka a aikin, inda rukuni na karshe suka kammala kwas a watan Maris da ya gabata.
Jama’ar gari ma ba su gamsu da wannan sabon kudiri ba, wani mai suna Simon Holdaway ya rubuta a shafinsa na Tweeter cewa: “Gaza gano matsalolin da Hukumar ’Yan sandan birnin Landan take fuskanta abin ban mamaki ne,” yayin da wani ya rubuta: “Shi ke nan mahaukta sun amshe ’yan gudun hijira.”
Kwamishinan ’Yan sandan Birnin Landan Sa Bernard Hogan-Howe ya ce: “Mun san kusan harsuna 300 ake amfani da su a birnin. Muna bukatar mu dauki ’yan sanda da suke jin harsuna biyu a yankunan da ake amfani da harsunan. Na yi imani hakan zai karfafa amincewa ya taimaka wajen magance aikata laifuffuka da samun nasarar taimaka wa wadanda aka yi wa ta’asa ko shaidu.”
Wani Kakakin ’Yan sandan Birnin Landan ya ce, “Sakamakon dimbin harsunan da ake magana da su a Landan mun fahimci wasu daga cikin wadanda ake yi wa ta’asa da shaidu da sauransu da kan iya zuwa wurin ’yan sanda, ba lallai ne su iya Ingilishi sosai ba.”