Yarbawa sun fi mutanen Arewa ba da gudunmawar dukiya ga addini – Ustaz Hakimi
Ustaz dalhatu Abubakar Abdullahi Hakimi Kantana shi ne Shugaban Majalisar Malamai ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa reshen Jihar Legas. A tattaunawarsa da wakilinmu ya ce a shekara 24 da ya yi yana aikin da’awar addinin Musulunci a Jihar Legas, ya lura cewa al’ummar Yarbawa sun fi mutanen Arewa bayar da […]
Ustaz dalhatu Abubakar Abdullahi Hakimi Kantana shi ne Shugaban Majalisar Malamai ta kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta kasa reshen Jihar Legas. A tattaunawarsa da wakilinmu ya ce a shekara 24 da ya yi yana aikin da’awar addinin Musulunci a Jihar Legas, ya lura cewa al’ummar Yarbawa sun fi mutanen Arewa bayar da gudunmawar dukiya wajen yada addinin Musulunci:
Aminiya: Mane ne takaitatcen tarihin Malam:
Ustaz dalha: To, an haife ni ne a garin Kantana da ke karamar Hukumar Tafawa balewa a Jihar Bauchi. Na yi makarantar firamare a garin daga nan na yi sakandare a garin Kafin Madaki da ke jihar. Sai na zo garin Jos na yi makarantar School for Higher Islamic. Daga nan ne a 1994, marigayi Sheikh Isma’ila Idris ya tura ni Legas, domin in je in yi aikin karantarwa. A garin na Legas Allah Ya ba ni damar shiga Jami’ar Jihar Legas kara karatu. Na rike shugaban wannan kungiya na shiyyar Agege da sakataren kungiyar na Jihar Legas. Kuma a yanzu ni ne Shugaban Majalisar Malamai ta kungiyar ta Jihar Legas. Ina rike da wannan matsayi kamar shekara 18 da suka gabata. A takaice na yi shekara 24 a nan Jihar Legas ina aikin da’awa da wa’azi da karantarwa. Ina da mata uku da ’ya’ya da dama.
Aminiya: Daga lokacin da aka nada ka shugabancin wannan kungiya reshen Jihar Legas zuwa yanzu wadanne nasarori ne kake ganin an samu?
Ustaz dalha: Babu shakka mun samu nasarori masu yawa a Jihar Legas. Domin a lokacin da na zo Legas wannan kungiya ba ta da masallacin Juma’a ko daya. Amma yanzu ko a Unguwar Agege kawai muna da masallatan Juma’a uku. Haka muna da masallatan Juma’a a Apapa da Ali Mosho kuma muna duba yiwuwar bude wasu masallatan a wasu wurare a wannan jiha. Haka a lokacin da na zo a zauruka mutanenmu suke karatu, domin ba mu da makarantu. Amma a yanzu muna da babbar makaranta ta School for Hihger Islamic mai ajujuwa takwas. Bayan wannan muna da wata babbar makaranta mai ajujuwa 14 a Unguwar Apapa.
Aminiya: Yaya za ka kwatanta yanayin yadda aikin wa’azi yake a Kudu musamman yankin Yarbawa da kuma Arewa?
Ustaz dalha: Kamar inda muke a zaune wato yankin Yarbawa yawancinsu Musulmi ne. Kuma suna gudanar da aikice-aikace na addini. Sai dai tsarinsu yana da bambanci da irin namu tsarin. Don haka maganar wa’azi suna yi gwargwadon hali, saboda haka aikin da’awa a Kudancin kasar nan yana ci gaba. Amma an fi karfafa aikin da’awa a Arewacin Najeriya.
Aminiya: To, yaya za ka kwatanta yadda jama’a suke karbar da’awa a tsakanin Arewa da Kudu?
Ustaz dalha : Jama’ar da ke Arewa an dade ana yi musu wa’azi kuma akwai mutane masu dimbin yawa wadanda suke karbar wannan wa’azi. Sai dai kuma jama’ar Kudu sun fi bayar da gudunmawar dukiya wajen taimaka wa harkokin addini. Haka kuma su mutanen Kudu za ka dade ba ka ji ana rikici da su ba a kan harkokin addini. Domin su ba sa yarda a yi rikici a kan da’awa kamar yadda ake yi a Arewa.
Aminiya: Yaya yadda addinin Musulunci yake yaduwa a Arewa da kuma Kudu?
Ustaz dalha: Gaskiya idan ka lura mafiya yawan al’ummar Arewa Musulmi ne, haka a Kudu musamman yankin Yarbawa akwai Musulmi da yawa. Haka wadanda ba Musulmi ba, suna da yawa a yankin Kudu.
Sannan shigar Turawa yankin Kudu ya yi tasiri a harkokin rayuwar al’ummarsu. Amma duk da haka Musulmin da ke yankin Yarbawa, sun yi tsaye wajen kokarin karantar da harkokin addinin Musulunci. Don haka addinin Musulunci ya bunkasa a wannan yanki. Bayan haka akwai kabilun Ibo da dama da suke zuwa wajenmu suna karbar addinin Musulunci. Kuma kamar Hausawa da suke zaune a wannan yanki su ma suna iyakar kokarinsu kan harkokin addinin Musulunci. Saboda haka idan ka kwatanta yanayin yadda addinin Musulunci yake yaduwa tsakanin Arewa da Kudu, za mu iya cewa yankin Kudu sun fi kokari yada addinin Musulunci musamman talakawa.
Aminiya: To, yaya dangantaka take tsakanin Musulmi ’yan Arewa mazauna Kudu da kuma Musulmi ’yan kasa?
Ustaz dalha: A gaskiya dangantakarmu tana da kyau domin muna girmama juna kuma muna kokarin zaman lafiya a tsakaninmu. Kuma muna bai wa junanmu hakkokinsu kuma muna tuntubar junanmu da shawarwari. A duk lokacin da aka ji wani abu na damuwa a cikin al’ummarmu ya taso duk wadannan jagorori na addinin Musulunci na Arewa da kuma su Yarbawa a kan yi kokari a kirawo mu baki daya a zo a gaya mana matsalar da aka hango kuma a nemi shawarwari kan yadda za a warware wannan matsala.
Kuma ita da’awa kamar yadda a Arewa akwai ’yan Izala akwai ’yan darika, a Kudu ma akwai irin wadannan bangarori hatta a cikin Yarbawa suna da manyan malamai da suka yi karatu a kasashen Larabawa suka dawo da kyakyawar akida wadanda ake tare da su. Kuma a cikin Hausawan akwai ’yan darika wadanda suka yi zurfi a cikin darika haka kuma a Yarbawa ma akwai wadanda suka yi zurfi a cikin darikar. Amma babban abin da na fahimta wajen kishin addini da gina masallatai da makarantu da daukar dawainiyar ayyukan addini kamar a kafofin watsa labarai, Yarbawa sun fi mutanen Arewa kokari a wannan bangare. Kuma akwai kyakyawar dangantaka tsakaninmu domin duk abin da ake yi zai yi wuya ka ji an ce an yi fada tsakanin Yarbawa Musulmi dangane da addini. Wannan shi ya sa ma galibi wa’azozin da muke yi a matakin na jiha muna iyakar kokarinmu mu samu kwararren masani wanda yake jin harshen Yarbanci.
Aminiya: To a karshe wane sako kake da shi zuwa ga Musulmin da ke Kudu?
Ustaz dalha: Sakon da nake da shi zuwa ga al’ummar Musulmi musamman Hausawa da ke Kudu da sauran Musulmi baki daya, shi ne mu kara jin tsoron Allah. Jin tsoron Allah shi ne zai ba mu dauwammamen zaman lafiya kuma ya kawo mana karuwar arziki. Mu kiyayi duk abin da zai kawo rigima, mu yaki kabilanci. Kada Bahaushe ya zo ya ga ana fada da Bahaushe dan uwansa ya kama fada da Bayarabe ko wata kabila ba tare da ya yi bincike ba. Haka kada Yarbawa su samu wata kabila na fada da Yarbawa su shiga ba tare da bincike ba.