Yarbawa sun yi wa Hausawa fintinkau a fannin sana’a – Haruna Mai’agogo
Wani mai sayarwa da gyaran agogo a garin Apata kusa da Ibadan, Malam Haruna Muhammed wanda Sarautarsa ta Galadiman Apata ba ta raba shi da harkar kasuwancinsa ba, ya ce, kabilun Yarbawa suna rungumar sana’a ko aiki da hannu biyu sabanin Hausawa da suke yi mata rikon sakainar kashi. Galadima Haruna ya fadi haka ne […]
Wani mai sayarwa da gyaran agogo a garin Apata kusa da Ibadan, Malam Haruna Muhammed wanda Sarautarsa ta Galadiman Apata ba ta raba shi da harkar kasuwancinsa ba, ya ce, kabilun Yarbawa suna rungumar sana’a ko aiki da hannu biyu sabanin Hausawa da suke yi mata rikon sakainar kashi.
Galadima Haruna ya fadi haka ne a zantawa da Aminiya yana mai cewa, Yarbawa sun yi wa Hausawa fintinkau ta wannan fanni. “Haka kuma ba safai za ka gane talaucin Bayarabe ba, kuma za ka gan shi da nakasa a jikinsa amma yana yin wata sana’a ko aiki.
Amma Bahaushe babu wata nakasa a jikinsa da karfinsa za ka gan shi a kazance sanye da tsummokara da malfa a kansa yana dogara sanda a hannu yana yawon bara da suke zubar da kimar Hausawa da mutuncinsu a Najeriya da duniya baki daya,” inji shi.
Malam Haruna ya ce “Bangaren shugabanci daban bangaren sana’a daban, sai dai in tafi da su tare, domin da ruwan ciki ake jawo na rijiya. Kuma sana’a ko aiki yana hana shugabanni kwadayin abin hannun talakawansu.”
“Kishin mutanenmu shi ne ya sa muka amince da karbar wannan sarautu da muka sadaukar da kawunanmu da abin aljihunmu domin hada kawunan jama’armu da kare mutuncinsu tare da sanya su a mikakkiyar hanya a wuraren da suke zaune a wannan gari,” inji shi.
Ya ce “Yau shekara 30 ke nan da na fara saye da sayar da agogo kuma na fara ne da jari kalilan da bai wuce Naira dubu daya ba, kuma wannan harka kadai nake yi tun daga wancan lokaci zuwa yanzu. A kan riba kuwa sai godiya ga Allah domin wannan harka ce ta suturta ni. Dukan al’amuran da suka shafi rayuwata daga ribar sayar da agogo na samu. Wadannan yara biyu da ka gani a tare da ni a cikin kasuwa suna daga cikin ’ya’yana 8 da na auri uwayensu daga ribar agogo. Idan wadannan yara sun dawo daga makarantar boko ne suke zuwa kasuwa su taimaka mini wajen hulda da abokan ciniki masu saye da gyaran agogo.”