Yaren kauna: Yadda ake bayyanar da kaunar da ake cikin zuciya
Abubuwan so da kauna da ake yi ga wanda ake so da nufin bayyanar da so
Yaren kauna na nufin abubuwan so da kauna da ake aikatarwa da aiwatarwa ga wanda ake so da nufin bayyanar da so da kaunar da ake masa a cikin zuciya.
Soyayya irin ta tsakanin ma’aurata tana da yaruka guda biyar:
- Kyautata lokaci;
- Lagudar jiki;
- Kalaman tabbatar kauna;
- Kyautukan kauna; da kuma
- Ayyukan hidima.
In muka lura kusan kowane daga cikin ma’aurata na bukatar duka yaruka biyar din nan daga wajen wanda yake aure.
Amma sai dai kowanne akwai wani yare da ya fi ba wa muhimmanci sama da sauran wadanda in ya kasance wanda yake aure bai yi masa shi ba, to zuciyarsa ba za ta samu natsuwa ba, za ta yi ta kokwanto game da tabbatuwar wannan so da kaunar.
Kyautata lokaci
Wadansu ma’auratan, hanyar nuna musu so da kauna da nuna an damu da su shi ne abokin aurensu ya ba su lokaci mai inganci, ya kasance kuma a wannan lokaci daukacin hankali da tunani da shaukinsu gaba daya yana kan abin kaunarsu.
Masu irin wannan yaren kaunar suna so a saurare su, a maida hankali gare su, a yi musu maganganun nuna so da kauna da kulawa, a yi musu kallon kauna da murmushin karramawa.
Duk a yi musu haka ba tare da hankali da tunani ya dauke daga kansu zuwa wani abin daban ba.
In aka yi musu haka, zai taba zuciyarsu a mafi dacewar wurare, zai tausasa ruhinsu, ya sa su su ji sun zama ’yan lele masu muhimmanci.
In ana musu haka a-kai-a-kai, za su kasance kullum cikin soyayya ba za su taba jin kishirwar kauna da kulawa ba!
Amma in aka yi musu wani yaren kaunar ba wannan ba, to komai yadda aka kure da kyautata wancan yaren kaunar ba za su taba jin cewa ana so ko kaunarsu, in ba wannan aka yi musu ba.
Kullum za su kasance cikin kishirwar so da kauna da nuna kulawa daga abokin aurensu.
Yayin da ake ba abokin aure mai irin wannan yaren lokaci, yawa ba shi ne abin nufi ba da inganci ba.
Abin bukata shi ne hira mai inganci da kalamai na gaskiya masu inganci da murmushi mai inganci ba na dole ba da sauransu.
Abin takaicin shi ne hanyoyin sadarwar zamani sun yi barna ga wannan yaren kaunar ta yadda ana tare amma zuciya da tunani na cikin duniyar yanar gizo.
Don haka da yawa masu wannan yaren kauna suna zaman karancin bayyana kaunar da ake musu wanda ka iya haifar musu tsananin kadaici da bakin ciki da bai kamata su yi fama da shi ba.
Lagudar kauna
Ma’auratan da yaren kaunarsu ya kasance lagudar kauna, sun kasance mutane masu halin kyanwa, wato son jiki.
Suna so a rika yawan tattaba su da shasshafawa da runguma da laguda shi ne ke fassarawa gare su cewa ana son su ana kaunarsu kuma an damu da su.
In ba wannan aka yi musu ba duk wata hidima da kyauta da kyautatawa bai sa su ji an nuna musu so da kauna da kulawa.
Wannan shafa da laguda da taba fata da jiki ba yana nufin mai gauraye da sha’awa ko neman biyan bukatar sha’awa ba.
A’a, shafa da laguda ce ta nuna kauna da kulawa da kuma nuna wa abokin aure shi dan lele ne kuma na musamman.
Duk da cewa wannan yaren kauna shi ne mafi sauki wajen samarwa da aikatarwa, amma da yawan ma’aurata masu wannan yaren kauna suna zaman aure da kishirwarsa saboda yanayin al’ada ya sa sai lokacin ibadar aure kawai ma’aurata suke taba juna shi ma yawanci da an kare shi ke nan.
Shi kuwa wannan yaren kauna yana bukatar shafa da laguda ne marasa hadi da sha’awa kuma masu inganci ta yadda za a yi su a lokaci da yanayi mafi dacewa, sannan a yi su a lokacin da hankali da tunani suna kan wanda ake laguda.
A takaice dai shafa ce da ake gauraya ta da so da kauna da kulawa da kyakyawan shauki.
A lokacin da ma’aurata suke lagudar kauna, ana sakar da sinadarin so da kauna odytocin cikin jininsu wanda hakan zai kara musu shakuwa da so da kaunar juna a ma’aikatar hankalinsu.
Iri-irin hanyoyin bayyanar da wannan yaren kauna su ne: sumba da runguma da tausa da cakulkuli da dankwashi da tawaiwayi da kwalkwalar kunne da shafa sama-sama da shafa mai danko da sauransu.
Mafi alfanu a cikinsu shi ne laguda, laguda na nufin, daga kwance ko zaune ko ma tsaye, ma’aurata su kasance kusa da kusa, su matse juna sosai, sannan su rika tattaba junansu a wurare na musamman amma ban da wuraren da suke motsa sha’awa, hadi da ’yar karamar hira mai cike da kalaman kauna da nuna kulawa, koda sha’awa ta motso musu a wannan lokaci kada su ba ta kulawa har sai sun lagudu sun sha dumin juna kamar na tsawon minti talatin zuwa awa daya.
Sai mako na gaba insha Allah, da fatar Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a koyaushe, amin.