Yarfen siyasa ce a ce muna gaba da Buhari – Ali Wakili

Sanata mai wakiltar mazabar Bauchi ta Kudu daga Jihar Bauchi Malam Ali Wakili ya ce masu zarginsu da cewa suna yi wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari kafar ungulu suna yi ne domin yarfen siyasa don su bata su a idon jama’a.Sanata Ali Wakili ya bayyana haka ne lokacin da yake tattaunawa da wakilinmu a Abuja, […]

Yarfen siyasa ce a ce muna gaba da Buhari – Ali Wakili
Yarfen siyasa ce a ce muna gaba da Buhari – Ali Wakili

Sanata mai wakiltar mazabar Bauchi ta Kudu daga Jihar Bauchi Malam Ali Wakili ya ce masu zarginsu da cewa suna yi wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari kafar ungulu suna yi ne domin yarfen siyasa don su bata su a idon jama’a.
Sanata Ali Wakili ya bayyana haka ne lokacin da yake tattaunawa da wakilinmu a Abuja, inda ya ce, babu wani sanata dan Jam’iyyar APC da yake yi wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari zagon kasa. “Shugaba Buhari ya riga ya bayyana wa duniya cewa ba zai tsoma baki a harkar zaben shugabanninmu ba, kuma da muka zabi Sanata Bukola Saraki a matsayin shugaban Majalisar Dattawa ya aiko masa da sakon taya murna.” Don haka sai ya zargi wadansu da ya kira shaidanu da shiga da fita don su nuna tamkar akwai matsala a tsakanin bangaren Shugaban kasa da bangaren majalisa.
Sanata Ali Wakili wanda ya kayar da tsohon Gwamnan Jihar Bauchi Malam Isa Yuguda a zaben da ya gabata, ya ce, “Saboda mutane sun dauki Shugaba Muhammadu Buhari tamkar mahadi da saba masa tamkar saba wa Allah ne, sai wasu ’yan siyasa suke amfani da wannan dama wajen bata abokan siyasarsu don su lalata su. Duk wanda yake son lalata maka siyasa sai ya ce kana fada da Buhari.”
Ya ce a iya saninsa da zaman da suke yi da Shugaban kasa Muhammadu Buhari babu wata matsala a tsakanin Majalisar Dattawa da bangaren Shugaban kasa, mutane ne kawai ke yin yarfen siyasa suna bata sunan  sanatoci da ’yan majalisa.
Ya ce tunda aka kaddamar da Majalisar Dattawa a farkon watan Yuni babu wata bukata da Shugaban kasa Buhari ya gabatar masa ta bata lokaci a kai balle a ce ta ki. Ya ce suna aiki da bangaren Shugaban kasa cikin mutunci da girmamawa, Shugaba Buhari yana aike wa majalisa da takardar tare da ambatar Sanata Bukola Saraki a matsayin Shugaban Majalisar Dattawa a duk lokacin da bukata ta taso, “Misali ya turo da sunayen manyan hafsoshin tsaro da na neman bashi ga Jihar Edo da na wanke Kwamishinan Zabe daga Jihar Jigawa, kuma duk ga ya ambaci Sanata Bukola Saraki da shugaban Majalisar Dattawa kuma gare shi ya aiko, kuma duk mun amince saboda mun san Shugaba Buhari mutum ne da duk abin da zai nema babu wasa ko wargi a ciki,” inji shi.
Sai ya zargi wata jarida da kokarin haddasa rudu da bata sunan ’yan majalisar saboda biyan bukatar mamallakinta.