Yarima Abubakar Audu: Garma ta karye da sauran aiki

A ranar Lahadin da ta gabata ce al’ummar Najeriya suka wayi gari da wani labari mai daga hankali na rasuwar dan takarar Gwamnan Jihar Kogi a karkashin Jam’iyyar APC Yarima Abubakar Audu, a daidai lokacin da sakamakon zaben Gwamnan Jihar da aka gudanar a ranar Asabar ya fara fitowa kuma alamu suka nuna shi ne […]

Yarima Abubakar Audu: Garma ta karye da sauran aiki

A ranar Lahadin da ta gabata ce al’ummar Najeriya suka wayi gari da wani labari mai daga hankali na rasuwar dan takarar Gwamnan Jihar Kogi a karkashin Jam’iyyar APC Yarima Abubakar Audu, a daidai lokacin da sakamakon zaben Gwamnan Jihar da aka gudanar a ranar Asabar ya fara fitowa kuma alamu suka nuna shi ne zai yi nasara.
An yi ta rade-radin cewa marigayin ya rasu ne bayan da aka ce ba a kammala zaben ba, sai dai bayanan da aka samu daga baya, sun nuna cewa Yarima Audu ya rasu ne tunda asuba kafin a fitar da wannan sanarwa. Bayanai sun ce Yarima Audu ya fara rashin lafiya ne tun a ranar zaben bayan ya jefa kuri’a.
Babu shakka marigayi Abubakar Audu mutum ne tsayayye wanda za a dade ana tunawa da shi a siyasar Jihar Kogi da kuma Najeriya baki daya. Kuma ya rasu a daidai lokacin da ya sake yunkurowa domin sake mulkar jiharsa wanda shi ne Gwamnanta na farar hula na farko da na biyu.
An haifi Yarima Abubakar Audu ne a 1947, mahaifinsa shi ne marigayi Baba Audu Oyidi, Orego na Atta na Igala kuma Sarkin Ogbonicha-Alloma da ke karamar Hukumar Ofu a Jihar Kogi. Shi ne dan takarar Gwamnan Jihar Kogi a karkashin Jam’iyyar APC a zaben 21 ga Nuwamban bana.Ya taba mulkin Jihar Kogi a matsayin Gwamna har sau biyu.A karon farko ya yi Gwamna daga Janairun 1992 zuwa Nuwamban 1993, lokacin rikicin zaben 12 ga Yuni. Sannan da aka sake dawowa mulkin farar hula a ranar 29 ga Mayu 1999 ya mulki jihar zuwa 29 ga Mayun, 2003.
Yarima Abubukar Audu ya fara nema iliminsa ne a karamar firamare ta En’e da ke Alloma kafin ya kare a babbar firamaren En’e ta Ankpa. Daga nan ya zarce zuwa makarantar Dennis Memorial Grammar School da ke Anacha sannan ya wuce Kwalejin Jos Commercial College inda ya rubuta jarrabawarsa ta GCE.
Tsohon Gwamnan ya wuce Landan a tsakanin 1975 zuwa 1978 inda ya karanta aikin banki da harkokin ma’aikata da wasu kwasa-kwasai. Wakili ne a kungiyar Akantoci ta Duniya da ke Landan da kuma Cibiyar kwararru Masu Gudanar da Harkokin Masana’antu ta Najeriya.
Ya shafe shekara 25 yana aikin banki, a bankin First Bank da Starndard Bank, inda ya rike mukaman shugabanci a matakai daban-daban har zuwa 1991, inda aka nada shi Babban Darakta a bankin FSB International Bank PLC.
A shekarar 1986 Yarima Audu ya fara shiga harkokin mulki inda aka nada shi Kwamishinan Kudi da Tsara Tattalin Arziki na tsohuwar Jihar Benuwai, inda ya rike mukamin har zuwa 1988, lokacin da aka rushe kwamishinonin, inda ya koma First Bank of Nigeria PLC a matsayin Janar Manaja.
Lokacin da aka kirkiro Jihar Kogi a 1991, ya fada harkokin siyasa inda ya tsaya takarar Gwamnan Jihar a karkashin Jam’iyyar NRC kuma ya lashe zaben 1991, inda aka rantsar da shi a matsayin Gwamnan farar hula na farko a jihar a watan Janairun 1992.
A 1998 ya sake tsayawa takarar Gwamnan Jihar a karkashin Jam’iyyar APP, inda ya lashe zaben Gwamnan jihar aka rantsar da shi a ranar 29 ga Mayun 1999. Rawar da ya taka wajen gudanar da ayyukan inganta rayuwar jama’a da tattalin arzikin jama’arsa sun ci gaba da zama ababen misali. Wasu daga cikin manyan nasarorin da ya samu sun hada da gina wasu rukunan gidajen ma’aikata guda uku da suka kunshi gidaje 1,500 a Lakwaja da sake fasalin garin Lakwaja ta wajen samar da hanyoyi masu kwalta da wutar kan titi da shatale-tale masu kayatarwa da gina hanyoyin karkara da sauransu.
Ya kuma samar da wutar lantarki da kimanin kashi 75 cikin 100 ga yankunan karkarar jihar da kuma samar da ruwan sha ga kashi 50 cikin 100 na karkarar ihar.
Sannan a zamaninsa ne ya gina filin wasa na zamani da babban otel a garin Lakwaja.
Marigayi Gwamna Audu ya kuma jawo masu zuba jari zuwa jihar daga ciki har da kafa kamfanin siminti na Obajana.
Sannan kafa Jami’ar Jihar Kogi a garin Anyigba, wata manuniya ce ta hangen nesansa da ririta albarkatun jiharsa. An aza harsashin ginin jami’ar ce a ranar 30 ga Nuwamba, 1999 wata shida kacal da hawansa kujerar Gwamna, lokacin da tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya ziyarci jihar.
Sannan ya gina Kwalejin Kimiyya da kere-kere ta Jihar Kogi domin karfafa shirinsa na samar da ilimi. Sannan ya gina gidan talabiji da tashoshin rediyo da jarida mallakar jihar, tare da sake fasalin gidan Turawan mulkin mallaka na Lord Lugard zuwa Gidan Gwamnati na zamani.
Sauran nasarorin da marigayi Gwamna Audu ya samu sun hada da rukunin gidaje 250, wani filin wasa da Asibitin kwararru na masu ciwon ido da cibiyoyin kiwon lafiya 25 da sakandaren ’Yan Mata ta Gwamnati don musayar dalibai da bohul-bohul 350 da hanyoyin cikin gari masu tsawon kilomita 300 da sayo bas-bas 100 don tallafawa a fannin sufuri da kuma kammala aikin wutar lantarki 40 a yankunan karkara.
Ya sake tsayawa takarar Gwamnan Jihar Kogi a shekarar 2003, amma ya sha kasa a hannun dan takarar Jam’iyyar PDP Ibrahim Idris a wani abin da ake ganin an yi masa magudi ne a zaben.
Ya sake tsayawa takarar Gwamnan a shekarar 2007, nan ma aka kayar da shi ta hanyar magudi, inda kotun sauraren kararrakin zabe ta soke zaben da aka yi wa Gwamna Ibrahim Idris ta umarci a sake gudanar da zabe, nan ma aka sake kayar da shi.
A shekarar 2012 ya fafata da Kyaftin Idris Wada, inda ya sha kasa, kafin ya sake fafatawa da shi a zaben Nuwamba, kuma yana dab da lashe zaben ne aka wayi gari ya kwanta dama.
Kafin rasuwarsa Audu ya lashe zabe a kananan hukumomi 16 daga cikin 21, inda babban mai kalubalantarsa Idris Wada ya lashe kananan hukumomi biyar, Audu ya samu jimillar kuri’a dubu 240 da 867, yayin da Wada na PDP ya samu dubu 199 da 514. Wato akwai bambancin tazarar kuri’a dubu 41 da 353 da Audu ya ba Wada. Sai dai kuma kasancewar Hukumar Zabe ta kasa (INEC), ba ta kammala sako sakamakon zaben ba rai ya yi halinsa ga Yarima Audu, yanzu za ta jira Jam’iyyar APC ta sanar da ita a hukumance kafin daukar mataki na gaba game da matakin da za ta dauka kan zaben.
Wani abin mamaki a daidai lokacin da ake shirye-shiryen gudanar da jana’izar marigayi Yarima Audu, an rika yada jita-jitar cewa ya farfado daga mutuwar da ya yi. A karshe an yi jana’izarsa a kauyensu na Ogbonicha da misalin karfe 2:00 na rana kamar yadda addinin Musulunci ya tanada, inda limamin Ankpa Malam Abdulrahman Isa ya jagoranci yi masa sallah.
Daga cikin wadanda suka halarci jana’izarsa akwai tsofaffin gwamnonin Kano Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso da na Neja Injiniya Abdulkadir Kure da tsohon Gwamnan Benuwai Sanata George Akume da takwaransa na Edo Lucky Igbinidion.