Yarima Ali zai sake tsayawa takarar shugabancin FIFA
dan gidan Sarautar Jordan Yarima Ali Bin Al Hussein ya sake bayyana niyyarsa ta sake yin takarar Shugabancin Hukumar Wasan kwallon kafa ta Duniya (FIFA) a karo na biyu a shekaranjiya Laraba a Jordan.Yarima Ali da ke neman maye gurbin shugaban hukumar mai barin gado Mista Sepp Blatter, a watan Mayu da ya gabata ya […]
dan gidan Sarautar Jordan Yarima Ali Bin Al Hussein ya sake bayyana niyyarsa ta sake yin takarar Shugabancin Hukumar Wasan kwallon kafa ta Duniya (FIFA) a karo na biyu a shekaranjiya Laraba a Jordan.
Yarima Ali da ke neman maye gurbin shugaban hukumar mai barin gado Mista Sepp Blatter, a watan Mayu da ya gabata ya fafata da Sepp Blatter wanda aka zaba karo na biyar ya jagoranci hukumar.
Haka kuma shi ne mutum na uku da ya bayyana niyyarsa ta son zama Shugaban Hukumar FIFA a bayan Shugaban Hukumar kwallon kafa ta Turai, Michel Platini da kuma tsohon jami’in Hukumar FIFA, Chung Mong-joon.
Sepp Blatter ya amince ya sauka daga shugabancin Hukumar FIFA ne bayan da zargin cin hanci da rashawa ya mamaye hukumar.
Za a yi zaben wanda zai maye gurbin Blatter ne a ranar 26 ga watan Fabrairun badi.