Yarima Charles na ziyara a Najeriya

Dan gidan sarauniyar Ingila mai jiran gadon sarautar Birtaniya, Yarima Charles tare da gimbiya Camilla na ziyara a Najeriya a yau Talata. Basaraken ya sauka a Abuja, fadar gwamnatin kasar inda yake ganawa da mahukuntan Najeriya da sarakuna da shugabannin al’umma. Rahoton na bayyana cewa, yariman zai kai ziyara jihar Legas bayan ya kammala wadda […]

Yarima Charles na ziyara a Najeriya

Dan gidan sarauniyar Ingila mai jiran gadon sarautar Birtaniya, Yarima Charles tare da gimbiya Camilla na ziyara a Najeriya a yau Talata.

Basaraken ya sauka a Abuja, fadar gwamnatin kasar inda yake ganawa da mahukuntan Najeriya da sarakuna da shugabannin al’umma.

Rahoton na bayyana cewa, yariman zai kai ziyara jihar Legas bayan ya kammala wadda yake yi a Abuja.