‘Yarima da Maciji’

Barkanmu da warhakar Manyan gobe, tare da fatan ana lafiya. A yau na kawo muku labarin ‘Yarima da Macizai’. Labarin ya yi nuni ne ga babu cutar da ba ta da magani. A sha karatu lafiya. Taku: Amina AbdullahiAkwai wani Yarima a wani kauye wanda wata iskar maciji ta shiga jikinsa. Mahaifinsa ya yi iya […]

‘Yarima da Maciji’

Barkanmu da warhakar Manyan gobe, tare da fatan ana lafiya. A yau na kawo muku labarin ‘Yarima da Macizai’. Labarin ya yi nuni ne ga babu cutar da ba ta da magani. A sha karatu lafiya.

Taku: Amina AbdullahiAkwai wani Yarima a wani kauye wanda wata iskar maciji ta shiga jikinsa. Mahaifinsa ya yi iya kokarinsa domin nemo masa magani amma abin kullum sai cigaba yake babu sauki. Hakan ta sa mutanen kauyen suka shiga kyamar wannan Yariman.

Wannan hali da Yariman ke fuskantar na matukar bata masa rai sai ya yanke shawarar barin garin da dare domin zuwa wani gari don nemo magani.

Yarima na isa garin sai ya shiga yin bara don neman abinci.  Sannan Sarkin garin yana da wata yarinya mai kiriniya. Yawan kushe abubuwan da mahaifinta Sarki ke yi ya sanya Sarkin yin alkawarin aurar da ita ga maroki domin ta gane kurenta.

Ran nan Yarima na isa gidan Sarki don yin bara sai Sarki ya sanya ya auri’yarsa a kan dole. Yarima suka kama hanya da sabuwar amaryarsa inda ya ce bari ya kishingida a karkashin wata bishiya ita kuma ta shiga daji nemo abinci.

Tana dawowa sai ta ga macizai biyu suna yin musu. dayan na cewa ‘ka fita daga jikin yarima dayan kuma na cewa sai in har kai za ka fita”. Tana jin haka, sai ta zaro takobinta ta kashe su. Nan take Yarima ya samu lafiya.  Daga nan suka koma gida inda aka yi shagalin biki, kuma dukkan iyayensu suka yi farin ciki da haka.

Manyan gobe su gane cewa cuta ba mutuwa ba ce kuma akwai maganinta.