‘Yarima da Maciji’

Barkanmu da warhaka Manyan Gobe.   Tare da fatan alheri. A yau na kawo muku labari ne mai taken: ‘yarima da maciji’. Labarin ya kunshi yadda keta ta zama alheri ga wata yarinya ce ’yar gidan wani Sarki. A sha karatu lafiya. Taku: Gwaggo Amina Abdullahi Akwai wani Yarima a wani kauye shi kadai mahaifinsa ya […]

‘Yarima da Maciji’
‘Yarima da Maciji’

Barkanmu da warhaka Manyan Gobe.   Tare da fatan alheri. A yau na kawo muku labari ne mai taken: ‘yarima da maciji’. Labarin ya kunshi yadda keta ta zama alheri ga wata yarinya ce ’yar gidan wani Sarki. A sha karatu lafiya.

Taku: Gwaggo Amina Abdullahi

Akwai wani Yarima a wani kauye shi kadai mahaifinsa ya haifa kuma yana matukar kaunarsa. Ran nan sai makiya suka sanya masa maciji a cikin jikinsa. An yi, an yi a nemo wa yarima magani amma abin ya ki.
Ganin yadda sarki ya wahala game da shi sai Yarima ya yanke shawarar barin garinsu saboda bakin ciki.
A  garin da ya isa, Sarkin garin mugu ne ga kuma yawan auri- saki.  Akwai wata ’yarsa da ya tsana kuma ya yi wa  kansa alkawarin duk almajirin da ya zo neman abinci zai aura masa ita.
Rannan sai Yarima ya je gidan Sarki don rokon abinci, nan take Sarki ya aurar masa da ’yarsa.  Shi ko Yarima ya dauki amaryarsa suka tare a bakin kogi.
Da Yarima ya kwanta barci sai matarsa ta fita neman masu abinci. Tana dawowa sai ta ga katon maciji a bakin yarima da kuma wani macijin a gefensa, inda suka zama macijai biyu.
Nan da nan ta nemi wuka ta kashe macizan biyu. Da Yarima ya farka barci sai ta ba shi labari. Shi kuma ya ba ta labarinsa daga nan suka koma garin mijinta (Yarima) inda aka yi mata goma-ta-arziki.
Ashe auren da mahaifinta ya yi mata don ya muzanta ya zama alheri a gareta.
Manyan Gobe sai sati na gaba zan sake kawo muku wani labari mai dadi.