Yariman Bakura Barden Sunna
Idan Hausawa suka ce Barde suna nufin Jarumi, amma ba jarumin da ke turzawa inda ya ga babu rintsi ba. Jarumin da ke kutsawa ko a mutu ko a yi rai, mai dakakkar zuciyar da taron ‘yan adawa da magauta ba ya hana shi keta sansani ya wuce. To ko a musulunci akwai barade irin […]
Idan Hausawa suka ce Barde suna nufin Jarumi, amma ba jarumin da ke turzawa inda ya ga babu rintsi ba. Jarumin da ke kutsawa ko a mutu ko a yi rai, mai dakakkar zuciyar da taron ‘yan adawa da magauta ba ya hana shi keta sansani ya wuce. To ko a musulunci akwai barade irin wadannan, kamar dai Ahmad Sani Yariman Bakura da ya kutsa ya aikata wata sunna, wadda da yawa daga cikin ‘yan boko zalla da ‘yan sai mun ga bayan duk abin da ya saba wa fahimtarmu ke kokarin sokewa don son rai.
Allah Ya jikan Shehu Usmanu danFodiyo, a cikin sharhin littafinsa mai suna Ihya’ussunna… ya tabbatar da cewa: Mumini a koda yaushe yana cudanya da uzurra (Waton da ya ga al’amarin da ya sabawa fahimtarsa ko kuma yake ganin ba daidai ba ne, sai ya dauki bangaren uzuri ga wanda ya aikata abin) Shi kuma munafuki, babu abin da yake dubi face aibi.
Auren yarinya karama ‘yar shekara 13, al’amari ne mai rintsi har dai ga idanuwan jahilai da masu ilmi dz ke son gardama, da kuma wadanda ba su zauna gaban malamai suka karantar da su littafai daga farko zuwa karshe ba. To wannan ne ya sa Yarima fuskantar kalubale daga sassa daban-daban na kasar nan da wajenta, kasancewar ya auri ‘yar shekaru 13. Amma da yake shi barden sunna ne, kuma ya zauna makaranta gaban malamai, bai zamo dalibin yanar gizo ba, sai ya yi tsayinsa akan abin da ya tabbatar da gaskiya ne ba kuskure ba.
Wadannan mutane na ganin cewa cin zarafi ne ga manzo mai tsira da aminci a ce ya auri Nana Aisha (R.A) ( Wadda aka haifa shekara ta biyar da aiko manzon Allah mai tsira da aminci) da shekara tara, duk da riwayoyi da yawa da suka tuzgo akan wannan aurenkamar:
Buhari da ya ruwaito a hadisi na dubu 683 yana mai cewa: Khadija (R.A) ta yi wafati kafin hijira da shekara uku, sai ma’aikin Allah Ya auri Nana Aisha bayan shekara biyu ko kuma kusa ga haka, tana da shekara shida, ya tare da ita ta na da shekaru tara. Da kuma Abu Dawuda da Ya ruwaito a Kitabul Adab, cikinsahihinsa, hadisi na dubu da dari hudu da talatin da biyar. Kuma Ibn Sa’adin a dabakat, Juzu’i na takwas, shafi na 47: Daga Nana Aisha (R.A) ta ce: ‘’Manzon Allah SAW ya aure ni ina da shekaru shida, na tare ina da shekara tara.’’
Masu irin wannan ra’ayi, suna ganin yarda da ingancin wadannan hadisai, shi ke habaka wutar sukar da kafirai ke yi ga fiyayyen halitta, wanda a zahirin gaskiya ba haka ba ne. Auren Manzon Allah da
Nana Aisha ba shi kadai ne abin da suke suka ba. Kuma babban abin lura shi ne, addinin nan na Allah musulunci, ma’aikin Allah Annabi Muhammad ne Ya zo da shi kuma shi ne ya fi kowa sanin abin da yake daidai da kuma wanda ba daidai ba. Saboda haka babu abin da ke wajibin kowane musulmi face mika wuya ga duk abin da ya inganta daga manzon Allah koda ko mutum yana ganin akwai rintsi a ciki.
Suna kalubalantar don me manzon rahama zai auri mata fiye da hudu alhali shi ya hori mabiyansa da auren hudu! Shi ma wannan zagi hanyar kubu ce masa ita ce mu dage wajen karyata ruwayoyin
da suka tabbatar da cewa matanSa tara ne? Ko kuma zargin da suke yi na cewa Alkur’ani ya hori Annabi Muhammad SAW ya yaki mutane har sai sun yarda ba abin bauta da gaskiya sai Allah, hanyar kubuce masa ita ce mu yi mirsisi muce babu wannan a cikin addininmu?
A gefen sahabbai, Sayyidina Umar ya amince da Abubakar ya auri ‘yarsa Hafsa, alhali Abubakar (R.A) ya girmi Umar! Usman (R.A) Ya girmi Umar, amma Umar ya aurar da shi diyarsa, haka kuma Sayyidina
Umar (R.A) ya auri diyar imamu Ali (R.A), kuma duk duniya ta yarda cewa Sayyidina Umar ya girmi Imamu Ali, kuma kowa ya yarda an yi wannan auren. To su kuma me za mu ce? Ba su inganta ba? Ko kuma a daina fadi kada ace sun yi abinda bai dace ba. Idan dattijo ya auri sa’ar ‘yarsa, me muke cewa? Mun yarda da cewa wadannan mutanen kirki ne, kuma dole akwai wata kyakkyawar manufa da ta sa suka aikata hakan ya sanya ba ma jin wani dar-dar, sai muke ta karantawa yaranmu masu tasowa wannan kissar. Haka kissa da kuma Hadisan auren Nana Aisha. Duk abinda aka ce SAW ya aikata, mu mun san akwai wata hikima a ciki, ko mun fahimci hakan ko kuma ba mu fahimta ba, ko wasu sun zarge Shi akan lamarin ko ba su zarge shi ba, bayani zai zo cikakke akan hikimar wannan auren, wanda daga cikin hikimar ce ma ta sanya yau Yarima yake aure da matar da ya aura tun tana da shekaru goma sha uku. Sannan masu ganin cewar babu wani hadisi da ya inganta dangane da auren Nana Aisha a shekara tara, ba su da hujja ko ta sisin Kwabo.
Nasir Abbas Babi 08033186727