Yariman Gombe ya riga mu gidan gaskiya 

Marigayin shi ne babban Hakimin garin Gombe

Yariman Gombe ya riga mu gidan gaskiya 

Allah Ya yi wa Yariman Gombe da ke Jihar Gombe, Alhaji Abdulkadir Abubakar Umar, rasuwa.

Ya rasu ne da maraicen Talata dab da sallar Magariba a gidansa da ke unguwar Tudun Wada a Gombe.

Marigayin ya rasu bayan ya sha fama da doguwar jinya.

Kafin rasuwarsa, shi ne Yariman Gombe, kuma Babban Hakimin cikin garin Gombe da kewaye.

Kazalika, marigayi Baffa ne ga Sarkin Gombe, Alhaji Abubakar Shehu Abubakar III.

Ya rasu yana da shekara 77 a duniya, ya bar matan biyu da ‘ya’ya 19.

Za a yi jana’izarsa a ranar Laraba da misalin karfe 2 na ranar a kofar fadar Mai Martaba Sarkin Gombe, Alhaji Abubakar shehu Abubakar III.

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan

Tags