Yariman Saudiya ya rasu a hatsarin jirgin sama

Wani dan sarauta da manyan jami’an gwamnatin kasar Saudiyya da dama sun mutu a wani hatsarin jirgin shalkwafta a kusa da kan iyaka da Yemen, a cewar gidan talbijin din kasar. Gidan talabijin Al-Ekhbariya sun sanar da cewa Yarima Mansour bin Moqren, wanda shi ne mataimakin gwamnan lardin Asir, kuma dan tsohon yarima mai jiran […]

Yariman Saudiya ya rasu a hatsarin jirgin sama

Wani dan sarauta da manyan jami’an gwamnatin kasar Saudiyya da dama sun mutu a wani hatsarin jirgin shalkwafta a kusa da kan iyaka da Yemen, a cewar gidan talbijin din kasar.

Gidan talabijin Al-Ekhbariya sun sanar da cewa Yarima Mansour bin Moqren, wanda shi ne mataimakin gwamnan lardin Asir, kuma dan tsohon yarima mai jiran gado ya rasu.

Sai dai ba su fadi komai a game da halin da sauran jami’an gwamnati ke ciki, ko kuma sanadiyar hatsarin jirgin.

Wannan hatsarin ya zo ne a daidai lokacin kasar Saudiya ta kama wasu daga cikin jami’an gwamnatin kasar bisa zargin almundahana a wani shirin kasar na yin kakkaba da tsabtace shugabancin Saudiyya.

Hakanan kuma, a ranar Asabar ne, Saudiyya ta ce ta kakkabo wani makami mai linzami da aka harba cikin kasar daga Yemen, kusa da filin jiragen sama na Riyadh.