Yariman Saudiyya ya ragargaji Amurka kan sassaucin da ta yi wa Iran

Yariman gidan sarautar Saudiyya ya ragargaji Amurka kan sassaucin da ta yi wa Iran, bisa tattaunawar da gwamnatin kasar ta yi ta bayan fage, ba tare da sanin Gwamnatin Riyadh, sannan tana ruruta rikicin siyasa a Gabas ta Tsakiya.Yariman Turki al-Faisal, wanda dan uwa ne ga Ministan Harkokin Wajen Saudiyya, ya bayyana cewa Saudiyya da […]

Yariman Saudiyya ya ragargaji Amurka kan sassaucin da ta yi wa Iran

Yarima Turki al-FaisalYariman gidan sarautar Saudiyya ya ragargaji Amurka kan sassaucin da ta yi wa Iran, bisa tattaunawar da gwamnatin kasar ta yi ta bayan fage, ba tare da sanin Gwamnatin Riyadh, sannan tana ruruta rikicin siyasa a Gabas ta Tsakiya.
Yariman Turki al-Faisal, wanda dan uwa ne ga Ministan Harkokin Wajen Saudiyya, ya bayyana cewa Saudiyya da sauran kasashen da yankin Tekun-Fasha, sun cika da mamaki kan shirin difulomasiyya na sirri da Amurka ta kulla da kasar Iran.
Yariman ya ragargaji Gwamnatin Amurka ne a wata hira da ya yi da mujallar Wall Street, bayan an kamala wani babban taro kan harkar saro. Ya kuma soki lamirin Amurka kan irin rawar da taka a rikicin Siriya da ke yankin.
Shi ma Jakadan Saudiyya a Amurka, Yarima Mohammed bin Nawaf bin Abdulaziz ya soki lamirin Amurka kan yadda take tarairayar rikicin Siriya  a matsayin “caca ce mai tattare da hadari.” Don haka, a cewarsa, Saudiyya za ta iya tsayuwa da kanta wajen bayar da tsaro a yankin, ba tare da ta yi hulda d aYammacin Turai ba.
“Muna da tabbacin cewa tsare-tsaren Turai a kan Iran da Siriya yana tattare da hadari da barazanar tsaro a Gabas ta Tsakiya,” inji Jakadan Saudiyya a Amurka, kama yadda ya bayyana wa jaridar New York Times.