Yarinya Ese ta koma garinsu

A yanzu haka yarinyar nan ‘yar asalin Jihar Bayelsa mai suna Ese Oruru wacce ake zargin wani saurayinta dan asalin Jihar Kano mai suna Yunusa dahiru da “boye” ta koma gida a jihar Bayelsa bayan jami’an ‘yan sanda da ke hedkwatarsu a Abuja sun mika ta ga mahaifiyarta a shekaranjiya laraba.A yayin da shi kuma […]

Yarinya Ese ta koma garinsu
Yarinya Ese ta koma garinsu

A yanzu haka yarinyar nan ‘yar asalin Jihar Bayelsa mai suna Ese Oruru wacce ake zargin wani saurayinta dan asalin Jihar Kano mai suna Yunusa dahiru da “boye” ta koma gida a jihar Bayelsa bayan jami’an ‘yan sanda da ke hedkwatarsu a Abuja sun mika ta ga mahaifiyarta a shekaranjiya laraba.A yayin da shi kuma Yunusa yake tsare a wurin ‘yan sanda a Abuja har sai abin da bincike ya nuna.
Tun daga watan Agustan bara ne ake zargin Yunusa dahiru dan asalin garin Kura cikin Jihar Kano, wanda ake gudanar da sana’ar hayar keke mai kafa uku a Jihar Bayelsa da dauke Ese Oruru a garin Opolo da ke garin Yenegoa cikin Jihar Bayelsa, inda ya kai ta Jihar  Kano da niyyar ya aure ta.
A ranar Litinin din da ta gabata ne jami’an ‘yan sanda na ofishin ‘yan sanda na kasa shiyya ta daya suka je garin Kura suka kamo saurayin da budurwar. Wata majiya a ofishin ‘yan sanda na shiyya ta daya da ke Kano ta bayyana cewa budurwa Ese tana cikin koshin lafiya, kasancewar babu wata alamar damuwa a tare da ita.
Wannan al’amarin day a faru da wannan yarinyar ya sanya wadansu jaridun kudancin kasar nan suka himmatu wajen cakuda batun, inda suka ce Yunusa ya sato Ese ce kuma ya musuluntar  da ita da bad a son ranta bad a nufin ya aure ta. Sai dai kuma ita Es eta jaddada cewa ita ta biyo Yunusa zuwa Kano bisa radin kanta, bas hi ne ya tilasta mata ba.
A halin yanzu dai wadannan jaridun sun himmatu wajen ganin an hukunta matashi Yunusa da laifi sace Ese, amma abin tambaya shi ne, za a hukunta da laifi sace Ese ne ko kuwa da laifin taimaka mata ta bar  garinsu zuwa Kano?
A gefe daya kuma masarautar Kano ta nisanta kanta da rahotannin da wadannan  kafafen watsa labaran suka bayar cewa masarautar ta goyi bayan ‘boye’ yarinyar.
A karo na farko Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II ya shaida wa manema labarai cewa tun a watan Satumbar bara ne ya bayar da umarni ga Hukumar Shari’a ta Jihar Kano da ofishin ‘yan sanda na shiyya ta daya da ke jihar da su gudanar da shirye-shiryen da suka kamata don mayar da yarinyar hannun iyayenta.
Aminiya ta samu kwafin takardar da masarautar ta aike wa hukumar shari’a ta jihar a kan batun.  Tunda farko Hakimin Kura Alhaji Bello Bayero shi ya fara sanar da Sarkin Kano game da lamarin, inda a take Sarkin ya rubuta wa Hukumar shari’a don ta bincik i lamarin.  A wancan lokacin hukumar shari’ar ta bayar da shawarar cewa kamat ya yi yarinyar ta koma hannun iyayenta tunda ba ta kai shekara 18 da haihuwa ba.
Aminiya ta gano cewa bisa shawarar da Hukumar Shari’a ta bayar ya sa Sarkin Kano ya rubuta wa ofishin  ‘yan sanda na shiyya ta daya takarda inda ya umarce su da su mayar da yarinyar hannun iyayenta.
Sai dai kuma kwatsam a  ranar Litinin sai ga Hakimin Kura Alhaji Bello Ado Bayero ya shaida wa Sarkin Kano a fadarsa cewa an gano cewa kimanin kwanaki 4 da suka wuce budurwa Ese tana tare da saurayi Yunusa a garin Kura.

Kotu ce kawai za ta warware matsalar Ese – Aminu Daurawa
Kwamanda Janar na Hukumar Hisba Shaikh Aminu Ibrahim Daurawa ya karyata batun da ake yadawa cewa saurayi Yunusa dahiru ya boye budurwa Ese Oruru, inda ya bayyana gaba dayan lamarin a matsayin siyasa da kabilanci.
 “Lokacin da wannan yaro ya zo da yarinyar nan Kano sai da ya sanar da hukuma batun zuwan nasu. Babu yadda za a yi a ce wannan yaro sato yariyar nan ya yi, balle har kuma a yi batun boye ta. Shi dama ya yi niyyar zuwa ganin gida, ita kuma ta dage da cewa sai ta biyo shi tana so ta musulunta ta kuma aure shi. Wannan ya kore batun kwace ko satowa ko boye yarinyar da wani abu makamancin haka da ake zargin yaron da shi. Mu muna ganin an shigar da siyasa da kabilanci da addini a cikin lamarin.”
Shaikh Aminu Daurawa ya kara da cewa, “tun da farko lokacin da yaron ya zo da ita, bayan ya kai ta wurin mai unguwarsu, shi kuma ya kai su wurin Dagaci. Daga nan aka turo su fadar sarkin Kano. Bayan an  kawo mana ita Hukumar Hisba cewa za ta musulunta za kuma ta auri yaron. Sai muka tambaye ta shekarunta, a nan ta gaya mana cewa shekarunta 18. Sai muka tura su kotu ta yi takardar haihuwa. A nan muka ba ta takarda ta sa hannu cewa za ta musulunta don ra’ayin kanta ba don wani ya takura mata ba.  A yanzu haka takardar tana nan a fayil din da muka bude mata.”
Shaikh Daurawa ya bayyana cewa Hukumar Hisba ba ta yi komai da ka ba, sai da ta gayyato iyayen Ese inda suka bayyana ra’ayinsu game da musuluntar tata. “ Da yake mu a nan Hisba idan aka zo mana da irin wadannan abubuwa cewa an samu wata za ta musulunta, to mukan ce a nemo mana iyayenta. To a wanann karon ma haka muka yi, sai muka umarce su da su kirawo iyayenta. Da farko da suka zo iyayen nata ba su amince ba. Amma daga baya sai mahaifinta ya amince, inda ma ya tabbatar mana da cewa shekarun yarinyar 18, kamar yadda ta fada. Sai dai ita kuma mahaifiyar yarinyar ta bayyana cewa yarinyar shekarunta 14.’’
“Da muka samu sabanin zance daga iyayenta a game da shekarunta, sai muka nemi su kawo mana takardar haihuwarta. Idan ta kai shekara 18 shi ke nan tana da damar zabar addinin da take so. Amma idan ba ta kai haka ba, to dole a mayar da ita hannun iyayenta, zuwa lokacin da za ta cika shekaru 18 kamar yadda dokar kasa ta tanada.’’
“To ana cikin wannan tirka-tirka ne sai muka samu labarin cewa ‘yan sanda sun je Hukumar Shari’a da niyyar za su karbi yarinyar. Hakan ya sa muka damka ta a hannun ‘yan sanda wanda da kyar ta yarda ta bi su.’’
Har ial yau Daurawa ya bayyana batun cewa kotu ce kawai za ta iya warware lamarin gaba daya.” Ganin yadda aka mayar da batun sai muka gayyato lauyoyi Musulmi da su shiga batun don ganin ba a zalunci wannan yaro ba. Kasancewar ita yarinyar da kanta ta biyo shi ta kuma shiga Musulunci don ra’ayin kanta. Wani abu da zi kara tabbatar da gaskiyar lamarin shi ne, a lokacin da iyayenta suka zo, da farko kin yarda ta yi ta bi su, inda ta nuna cewa ita tana tsoron kada su tafi da ita su kashe ta sakamkon komawa musulunci da ta yi. Su ma iyayen nata da suka ga ta nuna rashin aminmcewa a kan bin nasu, sai suka hakura suka tafi suka bar ta a nan.  Wannan lamari duk a kotu za a warware shi, domin matukar ba canza wa yarinyar ra’ayi aka yi ba, ko kuma tsorata ta aka yi ba, na tabbata za ta yi bayanin duk abin da ya faru a gaban kotu.”

dana bai sace Ese ba – Mahaifin Yunusa
Malam dahiru Bala mazaunin kauyen Tofa a yankin kramar Hukumar Kura, shi ne mahaifin saurayi Yunusa,  ya bayyana cewa dansa ya fi shekara 10 yana tare da iyayen yarinya Ese a Bayelsa. “Yunusa shekarunsa na haihuwa 25. ya dauki tsawon shekaru 10 yana tare da iyayen Ese a Bayelsa. Da farko  sana’ar sayar da ruwa yake yi, sai ya zama shi yake kai wa mahaifiyar yarinyar  wacce ke sana’ar abincin sayarwa ruwa. Sun dade tare, sun san junansu sosai. Ba wai bako ba ne a wurinsu, domin ya zama dan gida a cikin zuriyarsu.”
Mahaifin Yunusan ya bayyana cewa, “A daren da suka zo Kano a gidana suka sauka. Bayan ya gaya min cewa yarinyar ta biyo shi ne tana so ta musulunta, sai na umarce shi da ya kai ta gidan Dagaci, daga nan ya tura su wurin Hakimi har suka kai gaban Sarkin Kano.”
Mahaifin Yunusa ya karyata batun cewa dansa ya boye yarinyar ne ya musuluntar da ita tare da niyyar aurenta, inda ya bayayna cewa shi da kansa ya yi iya kokarinsa wurin ganin yarinyar ta koma wurin iyayenta amma ta ki yarda ta bi mahaifiyarta. “Lokacin da mahaifiyarta ta zo har nana kauyen ta nuna tana so ta tafi da yarta. Ni na sa baki don yarinyar ta bi mahaifiyarta, amma walalhi kememe ta ki yarda ta bi mahaifiyarta ta. Ta ce ita tana tsoron abin da zai iya biyo baya idan ta bi ta can garinsu. Ganin wanann tirka-tirka ne ma ya sa na sake daukarsu na kai su wurin Hakimi domin a san yanda za a bullo wa maganar a hukumance.”
Duk da cewar mahaifin yaron ya bayyana cewa ya bar lamarin gaba daya a hannun Allah, amma duk da haka ya yi kira ga gwamnati da ta yi wa dansa adalci a kan wannan lamari. “Ni dai na bar gaba dayan lamarin a hannun Allah tun da yaron yana hannun hukuma. Haka kuma ina kira ga gwamnati da ta tabbatar an yi masa adalci, musamamn ganin cewa bai sato yarinyar ba,  haka kuma bai boye ta ba. Ita ce da kanta ta biyo shi.”
Binciken Aminiya ya gano cewa a tsawon watanni shida da Ese ta yi a garin Kura ba tare suke da saurayi Yunusa ba, ita tana hannun wani ne yaron Hakimin garin mai suna Malam Mukaddas Kura, wanda Hukumar Shari’a ta damka ragamar kula da yarinyar a hannunsa.
Wani mazaunin garin Kura mai suna Malam Muhamamd Sani, ya bayyana cewa,’a lokacin da Ese take hannun Malam Mukaddas a Kura mahaifiyarta ta zo wurinta amma kemem ta ki yarda ta bi ta. Tun wancan lokaci da mahaifiyarta ta koma Bayelsa ba mu sake jin duriyarta ba sai yanzu da maganar ta sake tasowa.’
Aminiya ta samu zantawa da wani abokin Yunusa dahiru mai suan Garba Yakubu, inda ya bayyana cewa Yunusa ya gaya masa cewa babu yadda bai yi da Ese a kan kada ta biyo shi ba, amma saboda son da take masa ta ki yarda da maganarsa har sai da ta biyo shi Kano.
Garba Yakubu ya kara da cewa, “Tsawon zaman da Ese ta yi a Kura ta zauna da mutane lafiya, domin tana cudanya da matanmu, haka kuma tana mutunta su kwarai da gaske. A wanann  lokaci ma har ta far koyon harshen Hausa.’’

Ba za mu yarda a hukunta Yunusa da laifin sace ta ba
– Lauya Huwaila
Barista Huwaila Muhamamd Ibrahim lauya ce mai faftukatun kare hakin bil’adama, ta shaida wa Aminiya cewa, daga tattunawar da ta yi da masoyan biyu ta fahimci cewa akwai karin gishiri a cikin gaba dayan lamarin, domin daga binciken da ta gudanar ta gano cewa saurayin bai boye yarinyar ba kamar yadda ake watsawa a kafafen watsa labarai.  “A gaskiya wannan yaro bai taho da yarinyar Kano da niyyar boye ta ba, duk da cewa tare suka zo Kanon, amma babu wata alama da take nuna hakan. ,Daga tattunawar da na yi da ita ta shaida min cewa ita ta nemi ta biyo shi Kano. Ita ce ma ta biya wa kanta kudin mota. Kuma har a yanzu da ake wanann tirka-tirka ta nuna cewa ba za ta koma garinsu ba. Domin a cewarta, da ta koma garinsu gara a kashe ta. Lokacin da aka takura mata ne ma  take bayyana cewa za ta iya komawa garinsu don tsoron kada a tsare saurayin nata.”
Barista Huwaila ta musanta batun da ake yadawa cewa budurwa Ese Oruru karamar yarinya ce da shekarunta ba su wuce 14 ba, inda ta ce, “daga ganin yarinyar ka san ta fi shekaru 16 da haihuwa. Kuma ba karamar yarinya ce da ba ta san me take yi ba. Ko batun musuluntar da ta yi, ta bayyana cewa ta yi ne bisa radin kanta ba wai tilast mata aka yi ba. Haka kuma zuwa yanzu ta fara sanin  abubuwa da dama da suka shafi addinin Musulunci. Tana sallolinta biyar, takan sanya hijab da sauran abaubuwa na Musulunci.” Inji ta.
Lauyar  ta ce za ta ci gaba da bibiyar  lamarin har sai ta ga an tabbatar da adalci. “ Tunda farko na shiga wannan kes din ne  da niyyar taimaka wa yarinyar, musamamn idan aka yi duba da karancin shekarunta, akwai matsala wajen ta iya tunkarar abubuwan da ke gabanta. Duk da cewa a yanzu hukuma ta karbi kes din, amam hakan ba zai sa mu nade hannumu wuri guda ba,  za mu ci gaba da bibiyar kes din har sai mun tabbatar an yi kowa daga cikinsu adalci. Haka kuma ina jadadda cewa idan har aka tuhumi Yunusa da laifin boye yarinyar kamar yadda ake fadi, ba za mu yarda da hakan ba. Domin ba za ka hukunta mutum da laifin da bai yi ba. Daga binciken da na yi, yarinyar da bakinta ta tabbatar ba shi ya matsanta mata ya taho da ita Kano ba. Ita ta nuna tana son ta biyo shi, don haka ba shi da wani laifi a kan biyo shi da ta yi Kano.”