Yarinya na zubar da hawayen tsakuwoyi a Yemen
A gundumar Yammacin Hodeida da ke kasar Yemen, wani uba, Mohammad Saleh al Jaharani, ya koka kan yadda idanun ’yarsa, Saadia ke zubar da hawayen tsakuwoyi, kimanin kwanaki 14 da suka gabata a Fabrairun bana, har ta kai ga ya kashe dubban kudin Riyal din Yemen a wurin likitocin gargajiya.“Na kashe YR dubu 50, kimanin […]
A gundumar Yammacin Hodeida da ke kasar Yemen, wani uba, Mohammad Saleh al Jaharani, ya koka kan yadda idanun ’yarsa, Saadia ke zubar da hawayen tsakuwoyi, kimanin kwanaki 14 da suka gabata a Fabrairun bana, har ta kai ga ya kashe dubban kudin Riyal din Yemen a wurin likitocin gargajiya.
“Na kashe YR dubu 50, kimanin Dirhami 870 (wato Naira dubu 34,800) a wajen neman magani. An kuma dauki hoton idanunta a asibitocin gida, likitoci sun ce ba su ga komai ba,” inji shi.
Hoton bidiyon Youtoube da tashar Talabijin ta Azal Tb da ke Yemen ya nuna yadda idanun yarinyar ke fitar da kananan tsakuwoyi, maimakon hawaye.
Sai dai a lokacin da yarinya ke kuka a wurin barcinta babu tsakuwa, sai dai hawaye. Mafi yawan tsakuwoyin da take fitarwa, ana ganinsu ne da yamma. Kuma kananan duwatsun ba sa cutar da ita.
Mahaifin wannan yarinya, yana da ’ya’ya 20 da matansa biyu suka haifa masa, amma duk da haka ya damu da ganin yadda idanun Saadia ke zubar da akalla kananan tsakuwoyi 100 a rana. “Babu wani daga cikin ’ya’yana da ya taba yin irin wannan,” inji shi.