Yarinya ta kashe mai koya mata harbi a Amurka
Wata yarinya ’yar kimanin shekara tara ta harbe wani mai koya mata harbi da karamar bindiga mai sarrafa kanta a jihar Arizona da ke kasar Amurka.Hatsarin ya faru ne lokacin da bindigar, samfurin Uzi, ta kwace daga hannun yarinyar ta kuma ci gaba da sarrafa kanta-da-kanta. Lamarin da ya sa harsashi ya samu mai koyar […]
Wata yarinya ’yar kimanin shekara tara ta harbe wani mai koya mata harbi da karamar bindiga mai sarrafa kanta a jihar Arizona da ke kasar Amurka.
Hatsarin ya faru ne lokacin da bindigar, samfurin Uzi, ta kwace daga hannun yarinyar ta kuma ci gaba da sarrafa kanta-da-kanta. Lamarin da ya sa harsashi ya samu mai koyar da ita, Charles bacca, mai kimanin shekara 39 a ka, wanda kuma ya mutu bayan da aka kai shi wani asibiti da ke kusa.
Kamar yadda BBC ta ruwaito , yarinyar dai na tare da iyayenta ne a wajen koyon harbin kuma iyayen na daukar hoton bidiyo a lokacin da abun ya faru.
Wani ma’aikaci da ke aiki da wajen koyon harbin mai suna Sam Scarmardo ya ce bai taba ganin irin wannan lamarin ba a tsawon shekara 12 da aka yi da bude wurin. “An bai wa ma’aikatan da ke ba da horo a wannan wuri horo ta yadda za su buya idan hatsarin irin wannan ya ta so,” inji shi.
Kodayake, masu aiko da rahotanni sun ce koyawa yara harba bindiga ba sabon abu ba ne a kasar Amurka. Kuma yawancin wuraren da ke koyar da hakan suna da tsauraran dokoki kan horar da yara harbi.