‘Yarjejeniyar sayar wa Matatar Dangote ɗanyen mai a farashin naira za ta ƙare a ƙarshen Maris’
A fahimci cewa yarjejeniyar sayar da ɗanyen mai a farashin naira ta wata shida ce, kuma da sharaɗin akwai man.

Kamfanin Man Fetur na Najeriya NNPC ya ce yarjejeniyar da ya ƙulla da Matatar Dangote domin sayar mata da ɗanyen man fetur a farashin naira za ta ƙare a wannan wata na Maris.
Sai dai kamfanin ce yana tattaunawa da Matatar Dangote domin tsawaita yarjejeniyar sayar mata da ɗanyen mai a naira.
- An hana tashe bana a Kano — Nalako
- NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da ke Shirin Faruwa A Fagen Siyasar Najeriya
Sanarwar ta NNPC na zuwa ne bayan wasu rahotonni sun ce kamfanin ya dakatar da sayar wa matatar mai a farashin naira, kamar yadda suka ƙulla yarjejeniya tun da farko.
Wata sanarwa da mai magana da yawun kamfanin Olufemi Soneye ya fitar a ranar Litinin ta ce ba haka lamarin yake, yana mai cewa sai a ƙarshen watan nan na Maris yarjejeniyar za ta ƙare.
“Ya kamata a fahimci cewa yarjejeniyar sayar da ɗanyen mai a farashin naira ta wata shida ce, kuma da sharaɗin akwai man, wadda za ta ƙare a ƙarshen watan Maris na 2025.
“A ƙarƙashin wannan yarjejeniyar mun sayar wa Matatar Dangote gangan miliyan 48 ta ɗanyen man fetur tun daga watan Oktoba na 2024 zuwa yanzu.
“A yanzu muna ci gaba da tattaunawa domin ƙulla wata sabuwar yarjejeniya,” in ji shi.
Masana na cewa idan NNPC ya daina sayar wa Matatar Dangote mai a naira hakan zai iya haddasa hauhawar farashin man, maimakon sauƙin da ake tunanin hakan ya jawo a baya-bayan nan.
Dangote da NNPC sun rage farashi a gidajen mai
A makon jiya ne NNPC ya rage farashin litar man fetur a gidajen mansa da ke faɗin Nijeriya kwanaki bayan matatar man fetur ta Dangote ta rage farashin man a gidajen sayar da mai masu alaƙa da ita.
Ɗaya daga cikin manyan dillalan man fetur a Najeriya ya tabbatar da cewa a yanzu “NNPC na sayar muna da man fetur ne kan naira 840 a Legas, sai kuma naira 875 a Calabar da kuma Fatakwal.”
Hakan na zuwa ne kimanin mako ɗaya bayan Matatar Dangote ta sanar da rage farashin litar man, inda mutanen Nijeriya ke sayen fetur ɗin cikin farashin da ya yi ƙasa da na NNPC a gidajen man da ke haɗin gwiwa da matatar.
Wannan ya sanya aka riƙa ganin dogayen layukan ababen hawa a gidajen man fetur ɗin da ke da alaƙa da matatar ta Dangote.
Farashin da Dangote ya sanar zai riƙa sayar wa dillalai abokan hulɗarsa shi ne naira 825 daga 890, ragin naira 65 ke nan kan kowace lita.
Karo na biyu ke nan kamfanin yana rage farashin man a watan Fabrairun 2025, abin da dillalan man suka bayyana da “abin a yaba.”
Rage farashin ya sa man na Dangote ya zama mafi rahusa idan aka kwatanta da wanda ake shigo da shi ƙasar daga ƙetare.