Yarjejeniyar tsagaita wuta ta soma aiki a Gaza
Isra’ila ta fitar da jerin sunaye da hotunan mutum 33 da ta ce su ne take sa ran za a saki.
Da misalin ƙarfe 9:15 na safiyar wannan Lahadin agogon GMT yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Hamas ta fara aiki a Gaza.
Sai dai da farko tsagaita wutar ta ɗan samu cikas bisa abin da Isra’ila ta ce sai Hamas ta fitar da jerin sunayen mutanen da take garkuwa da su waɗanda za a saki sannan yarjejeniyar ta fara aiki.
- Isra’ila ta sake fitar da sabon sharaɗin tsagaita wuta a Gaza
- Mutanen da gobarar tankar mai ta kashe sun kai 86 a Neja
Daga bisani ne kuma Hamas a shafinta na X ta saki jerin sunayen wasu mata uku da ta ce na cikin waɗanda za ta saki a zangon farko.
A wani saƙo da ta wallafa, Hamas ta saki sunayen wasu mata guda uku da ta ce za ta fara saki a wani ɓangare na fara aiwatar da yarjejeniyar da Isra’ila.
Matan su ne Romi Gonen da Emily Damari da kuma Doron Steinbrecher.
A nata ɓangaren, Isra’ila ta fitar da jerin sunaye da hotunan mutum 33 da ta ce su ne take sa ran za su kasance a zangon farko da suka haɗa da wanda ya fi kowanne ƙarancin shekaru.
Kfir Bibas shi ne mafi ƙarancin shekaru daga cikin waɗanda ake garkuwar da su yana ɗan watanni tara da haihuwa lokacin da aka ɗauke shi.
Sai kuma wanda ya fi kowa tsufa a cikinsu mai shekaru 86, Shlomo Mantzur.
Masu shiga tsakani wajen sasanta Isra’ila da Hamas da kafafen watsa labaran Isra’ila sun ce an miƙa jerin sunayen waɗanda Hamas ke garkuwa da su za kuma ta sake su.
Jerin sunayen ne dai ya janyo tsaiko ga fara aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wutar da ya kamata ta fara aiki da misalin ƙarfe 7:30 agogon GMT na ranar Lahadin nan.
Wani ɓangare na yarjejeniyar dai ya buƙaci dole ne a bayar da jerin sunayen mutanen da ake garkuwar da su da za a saki aƙalla awa 24 kafin lokacin da yarjejeniyar za ta fara aiki.
Sai dai kuma tunda farko Hamas ta ce dalilin da ya sa take jan ƙafa wajen bayar da sunayen waɗanda take garkuwar da su shi ne saboda “wasu ’yan matsaloli.”