Yarjejeniyar tsagaita wuta ta soma aiki a Gaza — Qatar

Za a kai ga kulla yarjejeniyar tsagaita wutar ta din-din-din a Zirin Gaza da yaki ya daidaita.

Yarjejeniyar tsagaita wuta ta soma aiki a Gaza — Qatar

Rokoki da aka harba zuwa Isra’ila daga Gaza ranar Litinin 9 ga Oktoba, 2023. (Hoto: Reuters/Saleh Salem)

Yarjejeniyar tsagaita musayar wuta tsakanin Isra’ila da Hamas ta fara aiki a yau Juma’a da misalin karfe 7 na safe agogon Gaza kamar yadda gwamnatin Qatar da ke shiga tsakani ta bayyana.

Tsagaita bude wutar za ta fara ne da zaran Hamas ta saki wasu Yahudawa da take garkuwa da su da suka hada da mata da kananan yara, kuma hakan na zuwa ne bayan shafe tsawon makonni shida ana dauki-ba-dadi.

Bayan an dade ana tattaunawa kan tsagaita wuta, yarjejeniyar ta soma aiki, inda aka ji saukin rugugin bindigogi tun bayan harin ba-zata da Hamas ta kai wa Isra’ila ranar 7 ga watan Oktoba.

Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Qatar, Dokta Majed al Ansari ya ce, sun karbi jerin sunayen mutanen da za a fara sakin su da misalin karfe 4 na Asuba a wannan Juma’ar, yayin da ake sa ran Isra’ila ita ma ta saki Falasdinawan da ta garkame a gidan yari.

Kodayake yarjejeniyar tsagaita bude wutar ta wucin-gadi ce, amma ana sa ran za ta yi tasiri ta yadda za a kai ga kulla yarjejeniyar tsagaita wutar ta din-din-din a Zirin Gaza da yaki ya daidaita.

Gwamnatin Qatar na fatan cewa, ba za a sake samun jinkirin cimma yarjejeniyar ba, ganin cewa komai ya kammala a yanzu.

Wannan yarjejeniyar dai, za ta bada damar shigar da daruruwan motoci dauke da kayan agaji da suka hada da magunguna da man fetur cikin Gaza, inda kuma Isra’ila za ta kawo karshen luguden wutarta ta sama a yankin Kudancin Gaza.

Isra’ila ta kashe Falasdinawa 14, 854 a hare-haren da ta kwashe kwana 49 tana kaiwa a Gaza.

Haka kuma, fiye da Falasdinawa 7,000 sun bata ko kuma an binne su a cikin baraguzan gine-gine, a cewar hukumomi.