Yarjejeniyar zaman lafiya da ’yan bindiga ta faranta wa mazauna Birnin Gwari

Ƙaramar Hukumar Birnin Gwari da ta kwashe shekaru tana fama da  rashin tsaro a ’yan kwanakin nan hankulan al’ummar ya soma kwanciya a sakamakon yarjejeniyar zaman lafiya da gwamnati da jami’an tsaro da kuma shugabannin al’umma suka ƙulla da ’yan bindigar da ke addabar mutanen yankin. Wannan yarjejeniya ta kawo farin ciki da kuma shakku […]

Yarjejeniyar zaman lafiya da ’yan bindiga ta faranta wa mazauna Birnin Gwari

Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani (Hoto: Gwamnatin Kaduna)

Ƙaramar Hukumar Birnin Gwari da ta kwashe shekaru tana fama da  rashin tsaro a ’yan kwanakin nan hankulan al’ummar ya soma kwanciya a sakamakon yarjejeniyar zaman lafiya da gwamnati da jami’an tsaro da kuma shugabannin al’umma suka ƙulla da ’yan bindigar da ke addabar mutanen yankin.
Wannan yarjejeniya ta kawo farin ciki da kuma shakku a zukatan mutanen yankin na Birnin Gwari.
An shafe shekaru da dama ’yan bindiga na addabar mutanen yankin da ke zaune a ƙauyuka daban-daban, lamarin da ya yi sanadiyar rasa rayukan da dukiyoyi masu yawan gaske musamman gonaki tare da kuma tarwatsa wasu mazauna yankin daga garuruwansu.
Noma wanda shi ne babbar sana’a da al’ummar yankin ke dogaro da shi ya samu tsaiko a sakamakon hare-haren da ’yan bundiga ke kai wa manoma a gonakinsu.
Da yawansu dole ya sa suka dawo kusa da garuruwansu suna noma domin kaucewa harin ’yan Bindiga.
Sannan akwai manoma da yawa da ke hannun ’yan bindigar suna jiran danginsu su biya kudin fansa kafin a sako su.
Wasu daga cikin dokokin yarjejeniyar a cikin yarjejeniyar da aka sanya wa hannu sun nuna cewa ’yan bindigar na iya zuwa kasuwannin ƙauye sannan kuma su kai marasa lafiyarsu asibiti neman magani a garuruwan da suke ba tare da ’yan sa-kai na ƙauyuka ko mazauna ƙauyukan sun kai masu hari ba.
Sannan kuma suna da damar kai dabbobinsu kasuwannin domin cin kasuwa kamar yadda suka saba ba tare da cin zarafi ba.
Haka kuma a cikin yarjejeniyar, an nemi ’yan bindigar su daina karɓar haraji a hannun manoma ko mazauna ƙauyukan kafin su yi noma sannan su daina garkuwa tare da kai hari ga garuruwa ko lalata gonakin da ke yankin.
Kazalika, akwai buƙatar su bar mazauna ƙauyukan da aka tarwatsa su koma garuruwansu ba tare da kai masu hari ba.
Ra’ayin mazauna Yankin
Daya daga cikin shugabannin yankin Kwasakwasa mai suna Malam Abu ya bayyana cewa haƙiƙa an fara samun kwanciyar hankali a yankin su da ƙauyen Sabuwar Kuyello.
“Akwai yarjejeniyar zaman lafiya a yanzu kuma su makiyan muna ganinsu suna gudanar da al’amuransu babu tsamgwama a kauyuka.
“Ni kaina ina ganin su a yankinmu na Kwasakwasa suna tafiyar da al’amuransu na yau da kullum ba tare da an tsangwame su ba sai dai matsalar shi ne har yanzu dabbobinsu na mana ɓarna a cikin gonaki
“Hakan ya tilasta wa mutane girbe kayan amfaninsu tun ba su kammala nuna ba saboda kaucewa dabbobin da ke shiga suna masu ɓarna.
“Idan ka koka ga makiyayan wasu suna korar dabbobin amma kuma sai ka ga sun shiga gonar wani. Muna fatan za’a magance wannan matsalar saboda yarjejeniyar ta tabbatar,” inji shi.
Malam Abu ya kuma yi kira da a saki sauran mutanensu da ke a hannun ’yan bindiga a tsare tunda a yanzu an samu yarjejeniyar zaman lafiya duk kuwa da ya tabbatar da cewa a wasu ƙauyukan an samu labarin sakin wasu da ke tsare ba tare da biyan fansa ba.
Amma ya ce akwai wasu waɗanda aka fara cinikinsu a kan batun fansa kuma sai da aka biya aka sake su .
Shi ma Shagari wanda mazaunin Birnin Gwari ta tabbatar da cewa a yanzu mutane na zuwa gonakinsu har su yi dare ba tare da tsoro ba.
“A yanzu za ka ga mutanen mu na shiga gonakinsu da ke daji har su yi dare suna aikinsu  ba tare da wata matsala ba, a yanzu da muke wannan zancen da kai an sake buɗe kasuwar dabbobin kuma Fulani na zuwa cin kasuwar. Muna farin ciki da wannan nasara,” inji shi.
Shehu Abubakar Mashigi mazaunin yankin Kakangi ne wanda ’yan bindigar suka kora daga garinsa na asali ya ba da tabbacin cewa mutanen su a shirye suke su koma gidajensu idan suka tabbatar da tsayuwar yarjejeniyar.
Ya ce da Farko yana zaune ne a Mashigi kafin ’yan bindigar suka kore su inda suka koma Kasakaki kuma a can ɗin ma bayan shekaru biyu barayin dajin suka sake korar su.
“Yanzu ina zaune a Kakangi kuma a yanzu da aka samu wannan yarjejeniyar zaman lafiya ina fatan komai zai koma yadda yake saboda mu samu komawa gidajenmu domin burinmu kenan “inji shi.
Ya kuma yi kira da a samar da jami’an tsaro a yankin duk kuwa da yarjejeniyar zaman lafiya, inda ya ce hakan zai taimaka wajen ƙara tabbatar da zaman lafiya.
Alhaji Abubakar Birnin Gwari wanda ɗaya ne daga cikin shugabannin Fulani yankin Birnin Gwari ya tabbatar da cewa za a magance matsalar rashin tsaro a yankin.
“A Birnin Gwari aka haife ni kuma abin da ke faruwar a yankin nan ba mu jin daɗinsu” kamar yadda ya sanar a lokacin da yake jawabi a gaban Gwamna Uba Sani yayin da ya je buɗe Kasuwar dabbobi ta Kara bayan shekaru goma da rufe ta saboda matsalar tsaro.
“Gwamna ya ƙara haƙuri cewa wannan matsala za ta wuce kuma zaman lafiya zai samu a yankin Nan. Domin Babu wani matashin Fulani da zai gagaremu a nan ko a Kaduna domin duk wani da ke kasa da shekaru 50-60 a nan ya same ni,” inji shi.
Ƙalubalen da ake fuskanta
Duk da yarjejeniyar zaman lafiya wasu daga cikin mazauna yankin suna nuna shakku la’akari da abin da ya faru a shekaru bayan kasancewar an yi irin waɗannan yarjejeniyoyi amma suka rushe.
Wasu na nuna damuwa akan amincewa da kuma gaskiyar ’yan bindigar da kuma ko yarjejeniyar za ta karaɗe har da sauran garuruwan da ke makwabtaka da Birnin Gwari.
Ishaq Usman Kasai shugaba ne na kungiyar gamayyar garuruwar da ke kan iyakar Birnin Gwari da Jihar Neja, ya bukyaci a fadada yarjejeniyar ta haɗe da sauran yankunan.
“An yi yarjejeniyar a baya a wasu ƙauyukan Birnin Gwari da Katsina da Zamfara amma sun rushe.
“Amma a yanzu da wannan yarjejeniyar zaman lafiya wanda Gwamna Uba Sani da ofishin NSA da sauran jami’an tsaro da shugabanin al’umma suka shiga tare da wakilan ’yan bindigar muna fatan a samu nasara,” inji shi
Kasai ya ƙara da cewa “muna fatan alkhairi tare da yin addu’ar a samu nasara. Muna fatan duk waɗanda ke cikin yarjejeniyar za su rike amana.
“Muna son  kowa ya ji tsoron Allah domin bamu son yarjejeniyar ta rushe bayan Shekara ɗaya ko watanni shida kamar yarjejeniyoyin baya.
“Taron zaman lafiyar ya samu halartar wakilan ’yan fashin dajin irin su Yellow Jamboros wanda ke addabar yankin hanyar Birnin Gwari da Kwaga da Gayam da Palwaya da kuma Doka.
“Muna kira ga gwamnati da ta tabbatar da yarjejeniyar ta tsallaka sauran jihohi ba kawai a Birnin Gwari ko Jihar Kaduna kaɗai ba.
“Abinda zai kawo tabbataccen zama lafiya  shi ne a samu irin wannan zaman lafiya a jihohi dake fama da matsalar tsaro,” inji shi.
Kasai ya kuma bayyana amfanin kula da ’yan fashin dajin musamman waɗanda suka ajiye makamansu tare kuma da kulawa da sauran mutanen ƙauyuka da suka rasa dukiyoyinsu.
“Mun rasa ƙauyuka da garuruwa kusan 100 da ’yan bindiga suka tarwatsa a yankin Birnin Gwari. Mutanen yankin duk sun watse. Saboda haka akwai buƙatar gwamnati ta tallafa wa mutanen da suka watse,” inji shi.
Rawar da Gwamnatin Kaduna ta taka
Gwamna Sani ya ce zai yi adalci ga dukkan ɓangarori ba tare da nuna banbanci ba musamman ga manoma da makiyayan da ’yan kasuwa domin samun tabbacen zaman lafiya a jihar.
Ya bayyana cewa Jihar Kaduna tare da haɗin gwiwar sauran ma’aiktatun gwamnati  ce ta shirya tattaunawar zaman lafiyar da aka kwashe lokaci ana yi.
“Ta hanyar tattaunawar muka samu yarda da amincewar juna, inda manyan ’yan fashin dajin suka amince su ajiye makamansu suka kuma rungume zaman lafiya tare da magoya bayan su,” inji shi.
Ya ba da shawarar cewa akwai shirye shirye da ake yi domin samar da wasu shiri na gwamnatin jihar tare da kuma Gwamnatin Tarayya.
Gwamnan ya kuma gargaɗi ’yan fashin dajin cewa akwai tsarin da suka tanada na amfani da ƙarfi da kuma tsarin lalama.
“A lokacin da muke murna da karɓar waɗanda suka amince da zaman lafiya ba kuma za mu yi sakaka ba wajen maganin duk wanda ya ci gaba da addabar mutanen,” ini shi.
A jawabinsa, Sarkin Birnin Gwari Zubair Jibril Mai Gwari ya yi farin ciki da yarjejeniyar da aka samu tare da fatan hakan zai tabbatar da zaman lafiya a yankin.
Ya kuma yi fatan cewa a faɗaɗa yarjejeniyar zaman lafiya zuwa sauran yankunan da ke fama da matsalar tsaro.
“Mafi yawan masu addabar yankin nan a nan aka haife su mma daga baya sai suka zama wani abu na daban.
“Na yarda wakilan ’yan bindigar da gaske suke yi da yarjejeniyar nan saboda halartar taron da muke yi wnda ya kwashe kusan watanni shida.
“Idan Fulani ya zo maka da goro wajen taro abu biyu yake nufi ko zaman lafiya ko kuma ɗayan.
“Amma da suka halarci taronmu na ƙarshe suka raba goro wanda na ci kuma na raba wa mutane a wurin. Hakan ya nuna da gaske suke yi game da zaman lafiya,” inji shi.