Yaro dan shekara shida na hidima ga maifiyarsa don neman aljanna

Wani yaro dan shekara shida, daga kasar Pakistan, an hango shi a filin aikin hajji yana ta yi wa mahaifiyarsa hidima, tun lokacin da suka isa garin Mina.Yana rike da lema a saman kan mahaifiyarsa, don ya yi mata kariya daga kunar zafin rana, sannan ya mika mata wani kwali da take zama a kai […]

Yaro dan shekara shida na hidima ga maifiyarsa don neman aljanna

Wani yaro dan shekara shida, daga kasar Pakistan, an hango shi a filin aikin hajji yana ta yi wa mahaifiyarsa hidima, tun lokacin da suka isa garin Mina.
Yana rike da lema a saman kan mahaifiyarsa, don ya yi mata kariya daga kunar zafin rana, sannan ya mika mata wani kwali da take zama a kai duk sa’adda ta gaji. An ga wannan yaro yana ta kai kawo, wajen yi wa mahaifiyarsa hidima, duk da cewa ba ita ta sanya shi ba.
Yaron mai suna Mehyar, ya ce yana matukar son yin hidima tare da karrama mahaifiyarsa, tun lokacin da malaminsu na kur’ani ya tabbatar masa da muhimmancin aikin.
Ita kuwa mahaifiyarsa, wadda ake kira UmMehyar, ta ce ta taba zuwa aikin hajji a shekaru kadan da sujka gabata, tare da mahaifiyarta, wadda a halin yanzu ta rasu.
A lokacin ita kadai ce ‘yar da mahaifiyarta ta haifa, sai ta himmatu wajen yi mata hidima a lokacin aikin haji ko  a gida.
Ta ce ta tarbiyyantar da danta kyawawan dabi’u, kuma tana godiya ga Allah da ya sanya ta zo aikin haji tare da shi. Ta ce danta ya zaku da son ziyarar Makkah da Madina da manyan masallatai masu alfarma guda biyu.
Mehyar yana yawan tattaunawa da mahaifiyarsa kan darussan addinin musulunci, kuma ya bayyana mata cewa yana son shiga aljanna, al’amarin da ya ce malaminsa ya bayyana masa cewa hakarsa ba za ta cimma ruwa ba, ahr sai ya karrama mahaifiyarsa.

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan