Yaro mai cutar dukum ya zama kalandar tafi-da-gidanka

An samu wani  yaro mai cutar dukum a birnin Dubai, ta hadaddiyar Daular Larabawa, ya kasance mai lissafin shekara da kwanakin mutum a duniya cikin kankanen lokaci. Yaron ya san ranakun haihuwar abokan karatunsa da malaman makarantarsu da ma’aikatan makarantar.  Ganin yadda kwakwalwar Johann take haddace bayanai, ana ganin akwai yiwuwar ya shiga kundin tarihin […]

Yaro mai cutar dukum ya zama kalandar tafi-da-gidanka

An samu wani  yaro mai cutar dukum a birnin Dubai, ta hadaddiyar Daular Larabawa, ya kasance mai lissafin shekara da kwanakin mutum a duniya cikin kankanen lokaci. Yaron ya san ranakun haihuwar abokan karatunsa da malaman makarantarsu da ma’aikatan makarantar.  Ganin yadda kwakwalwar Johann take haddace bayanai, ana ganin akwai yiwuwar ya shiga kundin tarihin shahararrun al’amura na Guiness Book of Record.
Da aka tambayi Jonann Mendes ko shekararsa nawa, sai ya ce shekararsa 17 da watanni uku da kwana 14. Da kuma ya tattara su a tsarin lisafi, sai ya ce sun kai shekara 17 da rabi. Duk abin da ya gani tun daga kan kwanakin watan haihuwa da launukan tutar kasa da sunayen manyan biranen duniya, cikin minti daya yake dauke su a kansa.
“Wannan al’amari ya fara tun yaro yana dan shekara shida,” a cewar mahaifiyarsa Judy. “Yana matukar sha’awar kalanda; don haka yake nazarinta, ya zanata, sannan ya kwafi kwanakin watanni.”
Da farko Judy ba ta fahimci inda danta ya sa gaba ba, sai da wani kawunsa ya gan shi yana kwafar kalanda, sai ya fara tambayarsa game da kwanakin haihuwar zuri’arsu, kuma ya bayyana masa komai daidai.
“Daga nan baiwarsa ta ci gaba daga haddar kwanakin wata, zuwa kintace daidai da ranar da aka haifi mutum, har ma da yadda kwanakihn za su kasance a nan gaba,” inji Judy.
Don a tabbatar da wannan baiwa tasa, wakilin jaridar Gulfnews ya tamnbaye ranar da aka haife shi, da aka bayyana masa kwanakin watan, sai ya fadi rana da yadda za ta kasance a badi.
Ko yaya yake gudanar da wannan al’amari? Dangane da amsar wannan tambayar, Johann ya ce : “Na haddace lissafin kalanda, duk yana cikin kaina.”
Dangane da sunayen biranen duniya kuwa, cikin minti guda yake ambaton biranen duniya 50, tare da launukan tutocin kasashe fiye da 77. “Ina yin aiki tukuru a makaranta da gida, tuni na haddace sunayen manyan biranen duniya 152, yanzu abin da ya rage min in samu karin sunayen birane da tutoci masu yawa cikin minti daya,” inji shi.
Johannes na halartar makarantar Cibiyar kula da yara masu matsala a kwakwalwarsu (Dubai Centre for Special Needs (DCSN). Malamarsa Karen Menezes ta ce yana da sauri rike karatu, don haka ta bullo da wasu dabaru na bijiro masa da yawan tambayoyi.