Yaro mai manyan hannuwa na fama da kansa a kasar Indiya
Wani yaro dan shekara takwas da hannayensa ke ta kara zama dunduma-dunduma, ya jefa likitoci cikin rudani. Yaron mai suna Kaleem da ke kasar Indiya ba zai iya wasu ayyuka masu sauki ba, musamman abin da ya hada da daure zaren takalminsa. Domin girma da nauyin hannayensa sun fi kan jariri.Mahaifiyarsa, Haleema, ta bayyana cewa […]
Wani yaro dan shekara takwas da hannayensa ke ta kara zama dunduma-dunduma, ya jefa likitoci cikin rudani. Yaron mai suna Kaleem da ke kasar Indiya ba zai iya wasu ayyuka masu sauki ba, musamman abin da ya hada da daure zaren takalminsa. Domin girma da nauyin hannayensa sun fi kan jariri.
Mahaifiyarsa, Haleema, ta bayyana cewa ta fara ganin alamun girman hannayensa ne tun sa’adda da aka haife shi, amma babu abin da za ta iya yi a kai, ga shi yanzu har tsawonsu ya kai inci 13, tun daga wuyan hannu zuwa kan yatsu.
Wannan yaro ya koka kan yadda ake zaluntarsa, saboda ba ya iya daga hannuwan ya yi wasu ayuka masu saukin yi ga saurna yaran. Kuma ana nuna masa kyara, duk da cewa shi mai sha’awarar kwallon cricket ne.
“Wasunsu ma har dukana suke yi, ko su biyo ni da gudu za su kama,” inji shi.
Shi kuwa mahaifin Kaleem, Shamin dan shekara 45, fargabarsa ita ce, da wuya dansa ya zama mai cin gashin kansa, saboda wannan larura da ke tare da shi.
Likitocin Indiya sun kasa gane kan wannan cutar, kodayake wani daga cikinsu ya bayyana cewa da an tunkareta tun yana karami da an shawo kanta.