Yaro mai shekara uku ya fada rijiya a Kano

Yaron mai shekara uku ya fada a rijiyar ne a ranar Laraba.

Yaro mai shekara uku ya fada rijiya a Kano

Rijiyar da ta ci mutum hudu

An gano gawar wani yaro mai shekara uku da ya fada rijiya a unguwar Gaida da ke Karamar Hukumar Kumbotso a Jihar Kano.

Jami’in Hulda da Jama’a na Hukumar Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Saminu Abdullahi, ya ce lamarin ya faru ne da yammacin Laraba.

“Mun samu kiran waya daga wani mai suna Auwalu Muhammad da misalin karfe 4 na yamma a ranar Laraba.

“Sai muka hanzarta aika jami’an agaji zuwa wurin da misalin karfe 4.42 kuma an fito da gawar daga cikin rijiyar.

“An mika gawar ga mahaifin yaron, mai suna Musa Isa, don yi masa jana’iza,” inji shi.

Abdullahi ya ce ana binciken musabbabin faruwar lamarin.