Yaro ya hadiye mayen karfe 54 don yin gwaji
Yaron ya hadiye kunshin mayen karfe na farko a ranar 1 ga Janairu sai na biyu a ranar 4 ga Janairu 2021.
Wani yaro mai suna Rhiley Morrison mai shekara 12 da ke karatun kimiyya, ya yi kasadar kashe kansa ta hanyar hadiye mayen qarfe 54 don ganin ko zai iya samun sandar karfe a cikinsa, sannan yaya mayen karfen za su kasance idan ya je yin bahaya.
Yaron ya hadiye kunshin mayen karfe na farko a ranar 1 ga Janairu sai na biyu a ranar 4 ga Janairu 2021.
Wanda a karo na biyu suka ki wucewa ta makogoronsa.
Rhiley ya ta da mahaifiyarsa mai suna Paige Ward mai shekara 30 daga barci da misalin karfe 2:00 na tsakar dare yana fada mata cewa, ya yi kuskuren hadiye mayen karfe guda biyu.
Bayan yin hoton ciki na x-ray ya nuna cewa akwai wasu mayen karfe masu yawa da ya hadiya fiye da na baya.
Ya yi fargabar idan suka narke a cikinsa za su iya sanadin rasuwarsa.
Don haka ya yi gaggawar zuwa asibiti inda aka yi masa tiyatar awa shida.
Rhiley daga birnin Prestwich, Greater Manchester da ke kasar Birtaniya, ya kwashe kwana 10 bai iya zuwa ko’ina kuma bai yin amai saboda an sanya masa wani bututu da aka rufe bakinsa ta ciki yake iya cin abinci.
Paige ta ce, “Kaunar da Rhiley ke yi wa nazarin kimiyya ta yi zurfi kuma yana son yin gwaje-gwaje don haka ya gwada da kansa. Na yi qoqarin hadiye kwallayen mayen karfen don su hade a cikina, ta yadda za su iya zama wata sandar karfe a cikin tumbina.”
Abin mamaki, saboda halin yaranta Rhiley ya kwatanta yanayin hankalinsa na yaranta.
A nasa tunanin idan ya hadiye su za su iya fita ta wata siffar da ba yadda ya hadiye ba.
An sallami Rhiley daga asibitin bayan yin jinyar mako biyu. Kamar yadda mahaifiyar Rhiley ta sanar.
Paige ta ce “Wannan abin takaici ne na kallon yarona da ya bi wadannan matakai masu matuqar hadari, ina tunanin an kai wannan mataki ne sakamakon bullar annobar Kwarona da ta sa ba masu ziyartar yaron, abin tsoro ne a ce bai iya zama kuma yana cikin yanayin rashin lafiya kowane lokaci, saboda abin da ya hadiye na ta zagayawa a cikinsa.
Wani lokacin sai ya rike cikin a gurbin da ke yi masa ciwo, amma ba na jin dadin ganinsa a cikin wannan yanayi.
A lokacin da aka sa masa sirinjin allura a jikinsa, sai Rhiley ya bayyana wa mahaifiyarsa cewa, yana jin jikinsa kamar zai fashe.
Sai wata likita ta ce, ta taba jinyar wani yaro mara lafiya kamar Rhiley shi kuma a koyaushe mayen karfe yake hadiya.
Wani likita ya ce, ya yi wa wani yaro iyatar da ya fitar kwaya biyu kawai na mayan karfe ya hadiya, don haka Rhiley ya yi matuqar sa’a da ya rayu da guda 54 a cikinsa.