Yaron da matsafa suka kwakule wa idanu ya kama hanyar zama Farfesa
Yau kusan shekara uku ke nan, wato a ranar Lahadi, 4 ga watan Janairu, 2016, wasu mutane da ake zargin matsafa ne suka kwakule wa yaro dan shekara 4 da haihuwa idanu da karfin tsiya a Zariya, Jihar Kaduna. Yaron mai suna Abubakar Usman, wanda a bana ya cika shekara 7 a duniya kuma yake […]
Yau kusan shekara uku ke nan, wato a ranar Lahadi, 4 ga watan Janairu, 2016, wasu mutane da ake zargin matsafa ne suka kwakule wa yaro dan shekara 4 da haihuwa idanu da karfin tsiya a Zariya, Jihar Kaduna.
Yaron mai suna Abubakar Usman, wanda a bana ya cika shekara 7 a duniya kuma yake rayuwa a matsayin makaho, ya bayyana wa wakilinmu cewa babban burinsa shi ne ya zama Shaihin Malami, wato Farfesa, wanda dalili ke nan ya sa yake maida hankali ga karatu sosai.
Da Aminiya ta ziyarci gidan su yaro Abubakar Usman a Unguwar Bula, bayan asibitin Madarkaci Jushi Banzazau da ke Karamar Hukumar Zariya, Jihar Kaduna domin jin yadda yake rayuwa tun bayan da ya rasa idanuwansa, ya iske shi cikin koshin lafiya, inda kuma ya yi wa wakilin namu karatu da rubutu na boko da na ajami sannan kuma ya bayyana cewa:
“Yanzu haka ina karatu ne a makarantar ‘Professor International Zaria’ kuma ina aji biyu ne. Ina zuwa makaranta kullum ba fashi, a can nake cin abinci domin ba na dawowa da wuri. Ina da abokina mai suna Sani amma shi yana da idanu, ba kamar nib a, shi yana gani. Sunan malamina Ankul Ibrahim Mora, shi ma ba ya da idanu, ba ya gani kamar ni. Tare da shi muke yin karatu kullum a makaranta. Shi ne yake koya mini.”
Da Aminiya ta tambaye shi abin da yake so ya zama bayan ya kammala karatu sai ya ce, “ni ina son in zama Farfesa ne, in yi ta yin karatu da wasa da abokina Sani, wanda muke aji daya da shi, domin a makaranta tare muke karatu da wasa.”
Wakilinmu ya tuntubi mahaifin yaron mai suna Malam Usman Isa Auta domin jin irin kokarin da ake yi na kulawa da yaron sai ya ce: “Kwarai na gamsu da irin gudunmawar da jama’a suke bayarwa wajan ganin yarona Abubakar ya sami ingantacciyar rayuwa kamar kowane yaro, domin daga lokacin da abin ya faru har zuwa yau ban yi amfani da ko sisina ba wajan kula da lafiyarsa ko karatunsa ba, duk jama’a ke daukar nauyinsa har zuwa yau.
“Na farko, mai martaba Sarkin Zazzau Dokta Shehu Idris, shi ya dauki nauyin yaro wajen ganin cewa mun sami natsuwa da kuma kwantar mana da hankali da kokarin samar masa da lafiya. Domin har ma sai da ya ce idan za a iya maida wa Abubakar da idanu, shi a shirye yake da ya dauki nauyin yin hakan. Sai kuma na biyu, Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmed Elrufa’i shi ma ya yi kokari tare da alkawarin cewa zai dauki nauyin karatunsa har zuwa jami’a kuma ya ce yana nan a kan alkawarinsa da ya dauka ko bayan ya gama mulkinsa na gwamna. Haka ma wata baiwar Allah da ta ke zaune a Amurka mai suna Bawo, da ta dauki nauyin sanya Abubakar makaranta tare da kawo masa kayan karatu da kuma saya masa motar da za a rika kai shi makaranta. Kuma har zuwa yau tana ci gaba da kula da Abubakar. Ita ce wadda ta fara zuwa, ta yi kokari kwarai da gaske.
“Sai mutum na uku, Malam Isa Aliyu Fantami, wanda ya aiko masa da kayan karatu, musamman kwamfuta ta koyan karatun Alkur’ani mai girma. Shi ma a lokacin da ya zo daukar Abubakar wannan matar ta riga ta zo kuma har ya fara karatu; don haka shi ma yana tare da Abubakar har yanzu.”
Ya ci gaba da bayyana irin tagomashin da yaron ke samu, cewa “akwai wani makaho ma’aikacin gidan Rediyo Najeriya Kaduna mai suna Salihu Ibrahim, wanda ya kawo wa yarona kayan karatu irin wanda makafi ke aiki da su. Akwai tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Mukhtar Yaro, shi ma ya yi kokari.
Akwai Sanata Shehu Sani da Sanata Suleiman Usman Hunkuyi, kai da dai sauran mutane da dama. Haka kuma a yanzu akwai wani kamfanin waya mai suna Airtel, a yanzu su ne ke biyan kudin makarantar Abubakar. Don haka na gamsu da yadda rayuwar Abubakar ke gudana kwarai da gaske, kuma ina gode wa jama’a da irin gudunmowar da suka ba mu na ganin ci gaban Abubakar da wadanda na iya tunawa da su da ma wadanda ban iya tunawa da su ba.”
Hadiza Isa, ita ce kakar yaron kuma ta bayyana cewa: “To wasu na ta watsa labarin cewa wai Sadik ya mutu, to bai mutu ba kuma bari ma in fada maka wani abin mamaki da shi, tun daga lokacin da wannan abun ya faru da shi ko ciwon kai mai tsanani bai yi ba; a kullum wata sabuwar lafiya yake kara samu. Domin walwalarsa ta canza fiye da da.”
Ita ma mahaifiyarsa, Hauwa’u Usman, wadda a lokacin da abun ya faru ba ta samu damar tattaunawa da ita ba saboda firgici saboda ganin halin da danta ya shiga na rashin idanu ta hanyar da ba ta dace ba, yanzu ta yi bayani kamar haka: “A kimanin shekara uku da ta gabata, lokacin da aka kwakule masa idanu da karfin tsiya, na ga tashin hakali amma yanzu hankali ya kwanta. Mun bar wa Allah komai kuma rayuwarsa na tafiya cikin tsari fiye ma da da. Kuma basirar Abubakar ta karu, domin abin da yake yi yanzu a da ba ya yi. Ka ga dai yanzu yana gara taya kuma yana yin duk wani wasa da ’yan uwansa yara ke yi, kamar hawa keke, wasan buya, da dai sauran wasanni. Kai idan kana kallon wasannin da suke yi da sauran yara ’yan uwansa sai abun ya ba ka mamaki”
Hauwa’u ta kara da cewa, “abin da yake damu na wani lokaci shi ne, idan ’yan uwansa suna kallo talabijin sai ya koma gefe daya ya zauna. To, wannan shi ne yake ba ni tausayi, sai ya sa ina tunawa amma idan ba haka ba babu wani abu da yake damunsa kuma mun gode Allah da halin da muka sami kanmu a ciki na wannan jarrabawa da ya yi mana. Amma babu wani damuwa game da Abubakar kuma yana zuwa makaranta a kullum kuma idan sun tafi makaranta ba ya dawowa sai karfe biyar da rabi ake dauko shi a makaranta. To, in ya dawo ka ga ba wani sauran lokaci sai dai shirye-shiryen barci, domin an gaji. Don haka daga yin wanka sai Sallah sai kuma barci. Ka ji yadda ake rayuwa, don haka mun gode wa Allah.”
Malam Ibrahim Yusuf Mora Hunkuyi, shi ne malami na musamman da ke koya wa yaro Abubakar darussa a makaranta. Da yake amsa tambayar Aminiya dangane da burin yaron na zama Farfesa, ya bayyana cewa: “To, alhamdu lillahi, kamar yadda Abubakar ya ce yana da burin zama Farfesa, to a gaskiya a yadda muke ganin yana karatunsa, muna sa ran cewa ma idan akwai abin da ya fi ma Farfesa yana iya fin haka din. Sakamakon farko dai shi ne, samun gata da ya yi kuma da samun malami kwararre kuma da samun kayan aiki, ga kuma kulawa wadda shi ne abin da ya fi muhimmanci ga dalibi.
“To muna iya kokarinmu, Allah Shi ne shaidana cewar koda miliyan dari za a rika biyana a duk wata, misalin abin da nake koya wa Abubakar Sadik iya abin da zan iya koyar da shi ke nan, kuma in sha Allahu muna sa ran cewa nan da ’yan shekaru kadan masu zuwa Abubakar ya manta da wani abu da ake kira makanta, domin ma ko a yanzu ya fara mantawa da shi. To, ka ga kuwa tun da an fara samun irin wannan ci gaba muna sa ran duk abin da ya ce zai zama to zai iya zama a nan gaba. Wannan wani abu ne mai sauki a gare mu, in sha Allahu.”
Da yake kara bayanin yadda yaron zai cin ma burinsa na zama Farfesa, Malam Ibrahim ya ce: “Kuma hanyoyin da muke bi don ganin ya cin ma burin nasa na zama Farfesa shi ne kamar yadda na yi maka bayani a baya, cewa baya ga kasantowar kulawa da yake samu, sai kuma kulla kyakkyawar alaka da kai da wanda kuke tare da shi. A farkon saduwata da Sadik, na same shi yana cikin jin tsoron mutane saboda abin da ya faru da shi daga farkon rayuwarsa, don haka ba ya yarda da mutane. Amma a yanzu Sadik ya koma kamar ni na haifes hi, kuma ina cikin wadanda ya yarda da su a rayuwarsa fiye da yadda ba ka zato. Abu na biyu shi ne, muna amfani da dukkan nau’in kayan karatun da suka dace domin mu koyar da shi karatu don ya zama mutum cikakke, wanda ya sa muka mallaki duk wani nau’in kayan karatu nasa, baya ga wanda masu kaunarsa suka aiko masa da shi, domin tallafa wa rayuwarsa. Sai abu na uku shi ne, muna koyar da shi dabaru na tafiya da kuma dogaro da kai da kuma sanin duniya da kuma zama mutun cikakke kamar yadda kowa ke rayuwa. Domin yanzu idan ka ga Sadik cikin yara ’yan uwansa idan ba a ce ma Sadik ba ne ba za ka gane shi ba. Idan ba a fada maka cewa ba ya gani ba, ba za ka gane cewa ba ya gani ba, domin ba ya da dan jagora kuma duk inda za shi za ka gan shi da gudu za shi ba tare da jin tsoron komai ba. Yana wasa sosai cikin yara ’yan uwansa.
“Kuma wani abin mamaki da Sadik shi ne, kana rike hannunsa za ka ji ya kira sunanka cewa wane, ko kuma ya ce ga Ankul Mora ya shigo. To, ka ga idan muka ci gaba a haka, to muna sa ran cewa zai zama Farfesa in Allah Ya so.
“Kuma yanzu mun sami wani yaro wanda shi ma yana da matsalar ido, wanda shi ma ba ya gani. Mun hada su tare don ya san cewa ba shi kadai ne wanda ba ya gani ba kuma a kodayaushe za ka gan su tare sun hada kansu sun zama abokai. Ga shi ba ya da wata hayaniya ko kin ji, yanzu haka ina gaya maka cewa ya kusa haddace kusan Izifi 20, bangaran karatun Alkur’ani.”
A nasa bayanin, Babban-Daraktan makarantar, Dokta Jose Prasad Lawrence, wanda dan kasar Indiya ne, ya ce: “Abubakar Sadik yana da hazaka kwarai kuma babu wata matsala da muke fuskanta dangane da biyan kudin makarantarsa ko kuma rashin zuwa makaranta. Sai dai a baya ne muka dan fuslanci dan tsaiko wajen biyan kudin makarantarsa daga wadanda suke daukar nauyin karatun nasa amma yanzu kudin shekara suke biya, idan ya kare kuma su sake biya. Kuma yanzu haka yana da Izifin Alkur’ani wajen 20 a kansa da ya haddace tare kuma da fahimtar sauran bangarorin karatun da ake koyar da shi.”