Yaron da ya yi magana bayan wata hudu da haihuwa ya ce daga Mars yake

Wani matsashi dan Rasha mai sheekara 20, Boriska Mipriyanobich da ya yi ikrarin cewa daga duniyar ‘Mars’ yake kafin a sake haihuwarsa a duniya, ya rikita tunanin masana ilimin kimiyya saboda dimbin iliminsa a kan sararin samaniyya. Matashin ya ruda iyayensa da likitoci tun sa’adda aka haif shi, yayin da ya fara yin magana bayan […]

Yaron da ya yi magana bayan wata hudu da haihuwa ya ce daga Mars yake

Wani matsashi dan Rasha mai sheekara 20, Boriska Mipriyanobich da ya yi ikrarin cewa daga duniyar ‘Mars’ yake kafin a sake haihuwarsa a duniya, ya rikita tunanin masana ilimin kimiyya saboda dimbin iliminsa a kan sararin samaniyya.

Matashin ya ruda iyayensa da likitoci tun sa’adda aka haif shi, yayin da ya fara yin magana bayan wata hudu da haihuwarsa.

Jaridar Daily Mail ta ruwaito iyayensa na cewa yaron kan tattauna kan fannonin ilimin da su ba su sani ba, kamar ci gaban tsarin rayuwar boyayyun halittu, kuma ya fara karatu da rubutu da zane-zane tun yana dan shekara biyu.

“Alamar farko da ta nuna shin a daban ne, ta bayyana makonni kadan da haihuwarsa, inda ya rika tallafar kansa ba tare da taimko ba,” inji mahaifiyarsa.

Bporiska ya yi ikrarin cewa daga duniyar Mars’ an yi fama da musifar makaman nukiliya, inda ya ce mazaunann duniyar Mars wadanda tsawonsu ya kai kafa hudu, har yanzu suna zaune a karkashin jar duniya, kuma suna shakar iskar carbon diodide.

Ya ce rayuwar duniya za ta sauya da zarar an bankado sirrin mashahurin dodon Masar da gunkinsa na tarihi ke kafe a Giza, inda ya yi nuni da cewa mabudin al’amarin na bayan kunne.