Yaron gida ya shiga hannu kan yin luwaɗi da jikokin uban gidansa

Yaron ya ce wani ɗan uwansa ne ya koya masa wannan mummunar ɗabi’ar.

Yaron gida ya shiga hannu kan yin luwaɗi da jikokin uban gidansa

An kama wani matashi ɗan shekara 21, Mubarak Muhammad bisa zarginsa da yin luwaɗi da jikokin uban gidansa biyu da wasu ƙananan yara uku.

A wata hira da manema labarai a rundunar ‘yan sandan Sakkwato a ranar Litinin, wanda ake zargin ya bayyana cewar yaron gidan kakan yaran ne na tsawon lokaci.

“Tsawon watanni bakwai kenan nake cikin wannan lamarin, na yi wa jikan maigidana fyaɗe har sau uku kafin na yi wa jikan ƙanwarsa fyaɗe kusan sau biyar a lokuta daban-daban.

“Na yi wa wasu ‘yan uwan juna biyu fyaɗe da kuma wani almajiri guda ɗaya wanda ba zan iya tuna sunansa ba,” in ji shi.

Muhammad, ya ce yana yaudararsu ne ta hanyar su kawo masa ruwa.

“Idan sun kawo sai na ja su ɗakina na yi luwaɗi da su.

Ya ce abokin zamansa ne ya koya masa luwaɗi wanda ya kasance babban yayansa kimanin shekaru bakwai da suka wuce.

“A kan gado ɗaya muke kwana tare, akwai ranar dana taɓa tashi cikin dare sai na ga maniyyi a duburata.

“Na kai ƙara wajen mahaifinmu da ya raba mu, amma kimanin watanni bakwai da suka wuce ne na fara wannan haramtacciyar ɗabi’a da ƙananan yara.

“Amma yanzu na yi nadama, kuma na yi alƙawarin ba zan sake yin hakan ba idan aka sake ni,” in ji shi.