Yau ake mika sandar sarauta ga sabon Olubadan na Ibadan
Kwamitin hadin gwiwa na wakilan Gwamnatin Jihar Oyo da manyan fadawa a masarautar Ibadan sun tabbatar da cewa, a yau Juma’a da safe Gwamna Abiola Ajimobi zai mika sandar sarauta da satifiket, domin tabbatar da nada Cif Saliu Akanmu Olasupo Adetunji, a matsayin sabon Olubadan na 41.Kwamitin ya ce, babu wata takaddama a kotu dangane […]
Kwamitin hadin gwiwa na wakilan Gwamnatin Jihar Oyo da manyan fadawa a masarautar Ibadan sun tabbatar da cewa, a yau Juma’a da safe Gwamna Abiola Ajimobi zai mika sandar sarauta da satifiket, domin tabbatar da nada Cif Saliu Akanmu Olasupo Adetunji, a matsayin sabon Olubadan na 41.
Kwamitin ya ce, babu wata takaddama a kotu dangane da batun nada sabon sarkin, domin an yi aiki da tsarin karba-karba a tsakanin layin gidajen sarautu biyu da dokar nadin sarauta ta 1957 ta tanadar ne.
Da yake fadin haka a wajen taro da ’yan jarida a ranar Talatar da ta gabata, shugaban kwamitin, Dakta Lekan Balogun, ya ce: “Domin guje wa samun matsala, layin sarauta ya zo kansa, shi ne zai fito da dan takara da zai mika ga taron manyan fadawa da ba su cikin ’yan takara da za su duba cancantarsa da mika sunansa ga gwamnati.” Ya ce layi biyu na gidajen sarauta da mahukunta suka san da zamansu su ne layin Otun Olubadan da layin Balogun. A yayin da layin Otun Olubadan yake da mukaman sarauta guda 22 da ake hawa daga matakala ta farko da ake samun karin girma zuwa matakala ta karshe da ake haye wa zuwa karagar Olubadan. Shi kuwa layin Balogun ya kunshi matakala 23 ne da layuka biyun suke yin karba-karba wajen fito da sabon sarki. Ana yin amfani da wannan tsari ne tun kafuwar masarautar Ibadan zuwa shekara ta 1957 da aka yi wa tsarin kwaskwarima, domin dacewa da zamani.
Sabon Olubadan na Ibadan, Cif Saliu Akanmu Adetunji, dan shekara 87, ya fito ne daga layin gidan sarauta na Balogun kuma yana rike da sarautar Balogun na Ibadan ne zuwa yau da ya samu karin girma zuwa matakala ta gaba. A cikin shekara ta 1976 ne sabon Olubadan na Ibadan ya fara hawa mukamin sarauta na matakalar farko da aka nada shi a matsayin Mogaji na zuriyar Adetunji da ke unguwar Popo Yemoja a Ibadan, wanda ya rika samun karin girma zuwa yau da ya zama Olubadan na Ibadan.
Shugaban kwamitin tsare-tsaren bikin nada sabon sarkin da ake gudanarwa, a yau juma’a, Sanata Lekan Balogun, ya ce, kungiyoyi da kulob-kulob fiye da 200 na ’yan asalin Ibadan, a karkashin inuwar kungiyar Dattawan Ibadan (CCII) sun kammala irin nasu tsari domin bayar da gudunmawarsu domin kayatar da wannan gagarumin biki.
Birnin Ibadan shi ne birni na 3 mafi girma a Afirika da aka gina jami’a ta farko (Unibersity of Ibadan) da Asibitin koyarwa na farko (UCH) da gidan talabijin na farko (WNTb/WNBS) yanzu (NTA) da babban filin wasanni na farko (Liberty Stadium) da dogon gini mafi tsawo na farko (Cocoa House) da aka gina su a cikin masarautar ta Ibadan mai kunshe da kananan hukumomi 11. Za a rufe manya da kananan kasuwanni a yau Juma’a domin girmama wannan rana.