Yau ce ranar Sabuwar Shekarar Musulunci a Najeriya

A ranar Juma’a 21 ga Agusta 2020 ce Musulmi a Najeriya ke shiga Sabuwar Shekarar Musulunci ta 1442 Bayan Hijira Annabi Muhammada (SAW) daga Maka zuwa Madina. Da yake taya su murnar shiga Sabuwar Shekarar, Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhamad Sa’ad Abubakar III ya bukaci Musulmi su kara neman kusanci da Allah da kuma yawaita […]

Yau ce ranar Sabuwar Shekarar Musulunci a Najeriya

A ranar Juma’a 21 ga Agusta 2020 ce Musulmi a Najeriya ke shiga Sabuwar Shekarar Musulunci ta 1442 Bayan Hijira Annabi Muhammada (SAW) daga Maka zuwa Madina.

Da yake taya su murnar shiga Sabuwar Shekarar, Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhamad Sa’ad Abubakar III ya bukaci Musulmi su kara neman kusanci da Allah da kuma yawaita addu’o’i samun alherai da yayewar annobar coronavirus.

Ya kuma yi “kira ga Musulmin Najeriya da su ci gaba da wanzar da zaman lafiya da hadin kan ‘yan kasa”, ta bakin Mataimakin Sakataren Majalisar Harkokin Musulunci (NSCIA), Farfesa Salihu Shehu.

Tuni dai gwamnatocin wasu jihohi musamman a Arewacin Najeriya suka ayyana ranar Juma’ar a matsayin ranar hutun aiki domin taya Musulmi murnar shiga Sabuwar Shekarar.

Da yake bayar da hutun, Gwamnan Jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya taya al’ummar Musulmi murna da fatan samun kariyar Allah da albarkarSa.

Gwamnan ta bakin Shugaban Ma’aikatansa Sani Garba Shuni ya nemi mutanen Jihar Sakkwato su ci gaba da yin addu’ar samun zaman lafiya da ci gaban jihar da kasa baki daya.

A nasa bangare, Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje ya ayyana hutun ne a ranar Alhamis, inda ya bukaci al’ummar Musulmi a jihar da su daga da addu’o’in samun karuwar arziki da zaman lafiya da kuma ganin bayan annobar coronavirus.

Sarkin Musulmi Musulmi ya ayyana Juma’a 21 ga watan Agustan 2020, a matsayin ranar 1 ga watan Muharram na Sabuwar Shekarar 1442 Bayan Hijira.

Hakan ya biyo bayan umarnin NSCIA na cike watan Zhul Hajji kwana 30 saboda rashin samun rahoton ganin watan Muharammam a ranar Laraba 29 ga watan Zhul Hajji daga Kwamitin Duban Wata na Kasa.

Kashim Shettima zai jagoranci tawagar Nijeriya a taron MDD

NECO ta fitar da sakamakon jarrabawar 2024

Kano: Abba ya rusa ciyamomin riko

An haramta wa ma’aikatan Asibitin Tarayya yin ‘kirifto’ a wurin aiki