Yau ce Ranar Shan Fura ta Duniya

A Juma’ar nan, 13 ga Disamba ake bukin Ranar Shan Fura ta Duniya ta farko a tarihi.

Yau ce Ranar Shan Fura ta Duniya

Wasu Fulani na nuna al’adarsu a lokacin bukin kaddamar da rukunin gidajen

A Juma’ar nan ake bukin Ranar Shan Fura ta Duniya ta farko a tarihi.

Ƙungiyar Fulani ta Miyetti Allah Kautal Hore ta ayyana 13 ga watan Disamba a matsayin Ranar Shan Fura ta Duniya domin farfaɗo da kyawawan al’adun Fulani a Nijeriya da dama duniya baki ɗaya.

Aminiya ta ruwaito cewa Shugaban Ƙungiyar, Alhaji Bello Badejo, ya shaida mata a kwanakin baya cewa sun shirya tsaf domin kaddamar da bikin ranar wadda daga bana za a ci gaba da yi domin farfaɗo da kyawawan al’adu na Fulani.

“Za mu ƙaddamar da wannan buki ne a Kasuwar Shanu ta Maliya da ke Karamar Hukumar Karu ta Jihar Nasarawa.

“Kuma muna sa ran Fulani daga sassan Nijeriya da ma kasashen masu maqwbataka za su hallara domin gudanar da wannan buki na al’ada,” in ji shi.

Sai dai kuma bikin na zuwa ne a daidai lokacin da sojoji suke tsare da Bello Boɗejo wanda suka kama a gidansa a makon jiya, ba tare da sun bayyana dalilin kama shi ba.

Ana iya tuna cewa a lokacin da Bello Boɗejo yake wa Aminiya bayani kan Ranar Shan Fura ta Duniya, ya ce, “Fura jigo ce a al’adun Fulani, kuma a yanzu hatta waɗanda ma ba Fulani ba ne suna sha’awar ta, suna sha a matsayin abinci ko abun sha.

“Don haka wannan buki zai ba da gudunmawa sosai wajen wanzuwar hadin kai a tsakanin al’ummar Fulani da abokan zamansu a duk inda suke.”

Ya ce Fulani makiyaya a Nijeriya mutane ne masu dadadden tarihi, kuma a matsayinsa na shugaban ƙungiyar raya al’adun gargajiya na Fulani a kodayaushe, yana kokarin jaddada kyawawan al’adun Fulani, “domin abin da ake so a shugabanci shi ne bijiro da abun da zai bunkasa al’umma da kawo ci-gaba tare da dakile abubuwa marasa kyau.

“Fura jigo ce a al’adun Fulani, kuma a yanzu hatta waɗanda ma ba Fulani ba ne suna sha’awar ta, suna sha a matsayin abinci ko abun sha.

“Don haka wannan buki zai ba da gudunmawa sosai wajen wanzuwar hadin kai a tsakanin al’ummar Fulani da abokan zamansu a duk inda suke.”

Bello Bodejo ya kuma yi kira ga daukacin shugabannin kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore na jihohi da suyi koyi wajen farfado da al’adun Fulani su kuma tabbatar da hadin kai da zaman zaman lafiyar al’ummarsu.

A cewarsa, zai ci gaba da fafutukar wanke kashin kaji da aka goga wa al’ummar Fulani, a fadin qasar nan, domin Fulatanci yana nuna kawaici da kunya ladabi da kuma biyayya da bin doka, wannan ita ce al’adar Fulani ta asali, kuma ba za su gushe ba za su ci gaba da asassa wannan kyakyawar al’adar.

Gwamnatin Yobe ta tallafa wa magidanta 53,000 da N3.91bn a 2024

Uwargidan Sanata Goje ta tallafa wa mata da matasa a Gombe

An kama bokaye 2 kan zargin yi wa shugaban Zambiya asiri

Kirsimeti: FRSC ta aike jami’ai 1,539 zuwa Kano