Yau dalibai 33 za su karbi digiri mai daraja na daya a Jami’ar Ahmadu Bello
Shugaban Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya Farfesa Abdullahi Mustapha ya ce daga cikin zalibai dubu 14 da 67 da jami’ar za ta yaye a yau Juma’a 33 daga cikinsu za su karbi digiri mai daraja na daya (First Class) ne. Farfesa Mustafa ya bayyana haka ne a wajen ganawa da manema labarai da ya […]
Shugaban Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya Farfesa Abdullahi Mustapha ya ce daga cikin zalibai dubu 14 da 67 da jami’ar za ta yaye a yau Juma’a 33 daga cikinsu za su karbi digiri mai daraja na daya (First Class) ne.
Farfesa Mustafa ya bayyana haka ne a wajen ganawa da manema labarai da ya yi a ofishinsa don shirye-shiryen yayen daliban.
Shugaban jami’ar ya ce ba a ra’ayin jami’ar ba ne a ce ba ta son ba da digiri mai daraja na daya ga dalibai, a’a jami’ar tana kokarin tabbatar da sai wanda ya cancanta ne kadai zai samu digirin.
Shugaban ya ce daga cikin adadin, dalibai 1,273, za su karbi digiri mai daraja na biyu a babban rukuni, sai dalibai 2, 339 za su karbi digiri na biyu, sannan dalibai 360 su karbi digirinsu na uku.
Shugaban ya ce har ila yau akwai mutum daya da aka zaba da za a ba shi lambar girma ta Sardauna da sauran wadanda jami’ar za ta karrama da digirin girmamawa.
Farfesa Mustapha ya yi amfani da wannan dama wajen bayyana ci gaban da jami’ar ta samu a karkashin shugabancinsa wanda zai kare a watan Afrilun badi, inda ya kawo misali da aikin yashe madatsar ruwa ta Kubanni da ke makarantar wanda ya ce Gwamnatin Tarayya ta ba da kwangilarsa.
Shugaban ya ce aikin gina jami’ar kashi na biyu ma an sa harsashinsa da sauran aikace-aikace da tuni aka yi nisa a kansu.
Shugaban ya ce jami’ar tana iya kokarinta wajen ganin ta cimma burinta na samar da dukkan fasahar da za ta dace da zamani domin yanzu haka, akwai wadanda suka tashi tsaye wajen samar da fasahohi iri-iri a bangaren kyautata kiwon lafiya da noma da samar da iri da sauransu.