Yau Hisbah za ta gurfanar Murja Kunya a Kotun Musulunci
Hisbah ta cika hannu da Murja Kunya kan zargin sharholiya
Hukumar Hisba ta Jihar Kano te cafke shahararriyar ’yar TikTok, Murja Ibrahim Kunya, saboda zargin ayyukan badala.
Shugaban Rundunar ‘Kai da badala’ na hukumar Aliyu Usman, ya tabbatar mana da hakan.
A cewawrsa, “Jiya (Litinin) da yamma aka kama ta a gidansu da ke unguwar Tinshama bayan kusan awa uku muna fakon ta, sannan muka yi awon gaba da ita.
“Ana zargin ta da badalda, domin akwai wanda ake zargin kullum yana zuwa ya dauke ta da misalin karfe 10 na dare, sai 12 na dare ko 1 yake dawo da ita.”
- An kama su suna lalata a coci a hedikwatar ’yan sanda a Borno
- Albashin sojan Nijeriya N50,000 ne —Babban Hafsan Tsaro
A cewarsa, za gurfanar da Murja Kunya a gaban kotun Musulunci da ke unguwar PRP a yau Talata.
Aminiya ta ruwaito cewa Hukumar Hisbah na farautar mashahuran ’yan Tiktok akalla guda shida bisa zargin yada bidiyoyi badala a shafukansu na sada zumunta, lamarin da hukumar ta ce ya saba wa dokokinta.
Wannan na zuwa ne watanni kadan bayan babban kwamandan hukumar, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya gayyaci mata ’yan Tikto da ke Kano zuwa wani zama inda hukumar ta yi musu tayin tallafin sana’o’i da na karatu.