Yau Hisbah za ta yi zama da ’yan Kannywood
Jarumai da daraktoci da furodusoshin Kannywood sun bayyana takaici bisa sigar da Hisbah ta gayyace su zuwa ofishinta
A yau Litinin ne Hukumar Hisbah ta Jihar Kano za ta yi zamanta da ’yan Kannywood da ta gayyata zuwa ofishinta.
Gayyatar da Hisba ta yi wa daraktoci da jarumai da furodusoshi ya tayar da kura, inda wasu daga cikin ’yan masana’antar suka bayyana takaici bisa abin da suka kira kaskanci a yadda suka ji sanarwar gayyatar Hisbar ta gidan rediyo.
Shugaban kungiyar ’yan Kannywood, Alhassan Kwalle, ya ce ba su ji dadin gayyatar ba, kasncewa ba ta zo musu ta hannun kungiyarsu ko ta hannun hukumar tace fina-finai ta jihar ba.
Ahassan Kwalle ya ce ba karon farko ke nan da kungiyar za ta yi zama da Hisbah, kuma ba da wannan sigar ta saba gayyatar su ba.
- An cafke matar da ta sace ’yar shekara 3 a Neja
- MDD ta yi juyayin mutanen da Isra’ila ta kashe a Gaza
Ya ce a shirye suke su amsa kiran da hukumar ta yi musu, inda ya bayyana bukatar ta gyara kuskuren da ta yi.
Sai dai wata majiya a Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, wadda ta ce ba da ta izinin yin magana a hukumance, ta tabbatar wa Aminiya cewa hukumar ta aike wa ’yan Kannywood takardar gayyata zuwa zaman da ta shirya yi da su.
Wakilinmu ya nemi jin ta bakin Babban Kwamandan Hukumar, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa game da batun, amma ya shaida masa cewa yau za su yi zama da ’yan masana’antar ta Kannywood da aka gayyata.
Gayyatar wadda hukumar Hisbah ta ce ba ta shafi mawaka ba ne, ta zo ne bayan a makon jiya hukumar ta yi wani zama da ’yan TikTok a shirinta na ganin sun daina yada abubuwa marasa kan gado da suke yi a soshiyal midiya.
A yayin zaman na Hisbah da ’yan TikTok, ta gabatar musu da tayin daukar nauyin karatu ko aure ga masu bukata a cikinsu, ko ma ta ba su jari.
Wannan da daga cikin shirin da hukumar ta kaddamar da sunan Operation Kawar da Badala, da nufin kawar da ayyukan assha.