Yau INEC za ta ba wa Fintiri takardar shaidar cin zabe

INEC ta sanar da haka ne bayan a ranar Talata baturen zaben gwamnan jihar, Farfesa Mohammad Mele ya sanar cewa Fintiri ne ya lashe zaben.

Yau INEC za ta ba wa Fintiri takardar shaidar cin zabe

Ahmadu Fintiri

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta sanar cewa a yau Larabar da misalin karfe uku na rana za ta mika wa Gwamna Ahmadu Fintiri, takardar shaidar cin zaben da aka kammala ranar Asabar.

INEC ta sanar da haka ne bayan a ranar Talata baturen zaben gwamnan jihar, Farfesa Mohammad Mele ya sanar cewa Fintiri ne ya lashe zaben.

“Za a mika wa zababben gwamna da zababben mataimakin gwamna takardarsu ta shaidar cin zabe da misalin karfe 3 na rana,” in ji sanarwar da hukumar tafitar.

A ranar Asabar INEC ta karasa zabukan gwamnoni da na ’yan majalisun dokoki da ta ayyana a matsayin wadanda ba su kammala ba a lokacin da aka gudanar da farko.

Zaben Adamawa ya kasance cike da sarkakiya, inda kafin a tattara sakamakon kananan hukumomi 11 da suka rage, kwamishinan zaben jihar, Barista Hudu Yunus, ya sanar cewa Sanata Aishatu Binani ta Jam’iyyar APC ce ta yi nasara.

Daga baya hukumar ta yi watsi da sanarwar, ta sa a tsare shi a abincike shi, kafin daga bisani aka kammala tattara sakamakon zaben a ranar Talata.

Bayan kammala tattara sakamakon ne aka bayyana Fintiri a matsayin wanda ya yi nasara.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos