Abin da taron gaggawan kasashen Musulmi zai tattauna kan harin Isra’ila a Gaza

OIC za ta tattauwa washegarin da Isra’ila ta kashe Falasdinawa 500 a asibiti a Gaza,

Abin da taron gaggawan kasashen Musulmi zai tattauna kan harin Isra’ila a Gaza

OIC

A yau Laraba Kungiyar Kasashen Muslumi (OIC) ke yin taron gaggawa, bayan kwana 10 da gagarumin luguden wuta a kan Zirin Gaza.

Ana fata taron da zai gudana a kasar Saudiyya zai cim matsaya kan halin da ake ciki a yankin Falasdinawa, wadandan kawo yanzu akalla mutum 300 da ga cikinsu sun rasa muhallansu, baya ga rashin karancin abinci da rashin ruwan sha da wutar lantarki, a sakamakon hare-haren Isra’ilar.

Taron na OIC mai mambobi 57 na zuwa ne washegarin da jiragen Isra’ila suka kashe Falasdinawa sama da 500 a lokaci guda a wani asibiti a Zirin Gaza.

Za a yi taron ne a ranar da Shugaban Kasar Amurka, Joe Biden da ke goyon bayan Isra’ila, zai ziyarci Isra’ilar a kan rikicin.

Kawo yanzu Isra’ila ta kashe Falasdinawa sama da 3,000, ciki har da mata da kananan yara sama da 1,000, ta jikkata wasu dubbai a kwana 10 da ta shafe tana ruwan bama-bamai a Gaza, inda sojojinta ke shirin kaddamar da hare-hare ta ban kasa.

A ranar Lahadi ta kaddamar da hare-haren a matsayin martani ga harin da mayakan Falasdinawa na Hamas suka kai mata, inda suka kashe mutane 1,400, suka yi garkuwa da wasu 150.

A farkon makon nan ne Isra’ila ta yanke ruwan sha da wutar lantarki da man fetur a Gaza, ta kuma hana shiga da fita gaba daya daga yankin.

A ranar Talata, Shirin Abinci na Duniya (WFP) karkashin Majalisar Dinkin Duniya ta sanar cewa abincin da ya rage a yankin Falasdinawan ba zai wuci kwana biyar ba, inda a halin yanzu shagunan abinci ke rurrufewa saboda kayansu sun kare.

Kasashen Larabawa sun jima da kiran Isra’ila da ta fice daga Gaza tare da gargadin cewa abin da take yi na iya haddasa yaki a fadin yankin Gabas ta Tsakiya.

A ranar Talata, Iran ta bukaci ta bukaci Isra’ila ta fice daga yankin Gaza, ko kuma duk abin da ya biyo baya, ta kuka da kanta.

Rundunar Sojin Isra’ila ta umarci Falasdinawa su fice daga yankin Arewacin Gaza zuwa Kudanci gabanin samamen da za ta kai, amma ta tabbatar cewa har yanzu akwai dubbban daruruwan Falasdinawa da ba su fice ba.

Sai dai duk da hakan, a Kudancin Gazan ne Isra’ilar a kai harin da ya hallaka Falasdinawa kimanin 500 da ke zaman mafaka a wani asibiti, lamarin da ya ja mata karin la’anta daga sassan duniya.

’Yan Bindiga: An miƙa wa gwamnatin Kaduna mutum 58 da aka ceto

Sarkin Zazzau ya naɗa sabbin hakimai 7

Hajjin 2025: Maniyyata za su fara ajiye N8.4m a Kaduna

Barikin Ladi: Asalin garin da yanayin rayuwar mazauna