Yau Kotun Koli za ta ci gaba da shari’a kan wa’adin tsoffin kudi

Jihohi 12 sun maka Bankin CBN da Gwamnatin Tarayya a kotu kan haramta amfani da tsoffin kudin da aka sauya wa fasali

Yau Kotun Koli za ta ci gaba da shari’a kan wa’adin tsoffin kudi

Sabbin-takardun-kudi

A yau Laraba 22 ga watan Fabrairu, 2023 Kotun Kolin Najeriya za ta ci gaba da sauraron karar da jihohi 12 suka shigar gabanta na kalubalantar dokar haramta amfani da tsoffin takardun kudi da Gwamnatin Tarayya ta yi.

Aminiya za ta kawo muku rahoto kai-tsaye a safiyar yau daga Kotun Kolin game da wainar da ake toyawa a sharia’r.

Mako guda ke nan da kotun ta fara sauraron shari’ar da Gwamnatin Tarayya da Babban Bankin Najeria (CBN) da wasu jihohi biyu da ke goyon bayan tsarin, ke a matsayin masu kare kansu.

Tun a lokacin da aka shigar da karar, alkalan kotun guda bakwai karkashin Mai Shari’a John Okoro, suka ba da umarnin wucin gadi na aiwatar da dokar haramta amfani da tsoffin kudin, zuwa ranar da za ta fara sauraron shari’ar.

Tun a lokacin jihohin Kaduna da Zamfara da Kano suka yi kan gaba wajen ba da umarnin cewa a ci gaba da amfani da tsoffin kudin, wadanda a wancan lokacin wa’adin da gwamnati ta bayar shi ne, ranar 10 ga watan Fabrairu.

A lokacin da ta fara sauraron shari’ar a zamanta na ranar Larabar da ta gabata, 15 ga watan Fabrairu, ta umarci masu kara su hade uhume-tuhumensu a wuri guda, sannan ta sanya yau a matsayin ranar ci gaba da sauraron shari’ar.

Ranar da kotun ta yi zaman ne Majalisar Magabata ta Kasa ta yi zama inda ta bukaci bankin CBN ya samar sabbin kudaden a wadace ko kuma a ci gaba da amfani da tsoffin har zuwa lokacin da sabbin za su wadata.

Washegari kuma, a ranar Alhamis, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ba da umarnin tsawaita lokacin amfani da tsoffin takardun Naira 200 zuwa ranar 1 ga watan Afrilu.

Sai dai kuma ya umarci duk masu tsoffin takardun N1,000 da kuma N500 su kai su CBN ya ajiye musu a bankunansu.

A ranar Juma’a ’yan Najeriya a sassan kasar suka yi tsinke a rassan CBN domin ajiye tsoffin kudinsu, amma suka yi ta fama da matsaloli.

A ranar ce, bayan cikar kwari da CBN din ya gani jama’a sun yi a rassansa, ya ba wa bankunan kasuwanci umarnin su fara karbar soffin kudi daga hannun muane, matukar ba su haura Naira 500,000 ba, wadanda nasu a haura haka kuma, su kai rassan CBN.

Sai dai kuma sa’o’i kadan bayan nan murnar ’yan Najeriya ta koma ciki, inda bankin ya lashe amansa, ya janye umarninsa na farko. Hasali ma karyata sanarwar da ya fitar da farko bankin ya yi.

Sai dai kuma kawo yanzu, wasu bankunan kasuwanci na ci gaba da karbar tsoffin takardun kudin.

Dambarwar canjin kudi

Batun sauyin kudin dai ya haifar da suka ga gwamnati da kuma tarzoma inda aka yi asarar rayuka da dama a sassan Najeriya.

Ko a ranar Talata, Aminiya ta kawo rahoton an kona bankuna kimanin 10 a Jihar Ogun, baya ga wasu jihohi da aka samu irin hakan a kan batun karancin kudin da ’yan Najeriya ke fama da shi.

A gefe guda kuma, gwamnatocin Kaduna, Kano, Zamfara da sauransu, sun umarci mutane da su ci gaba da amfani da tsoffin kudin, tare da barazanar rufe duk cibiyar kasuwancin da ta ki karbar su.

Hakazalika, ana zargin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da yin kunnen kashi ga umarnin Kotun Koli, wajen kin amincewa a ci gaba da amfani da tsoffin takardun N500 da N1,000.

Gwamnonin APC sun ji dadi da umarnin kotun

Umarnin Kotun Kolin dai ya faranta wa bangaren Jam’iyyar APC da dan takararta Bola Ahmed Tinubu da ya fitar da sanarwar lale marhabun da umarnin Kotun.

Gwamnonin dai na zargin sauyin kudin wata manakisa ce da aka shirya domin kayar da jam’iyyarsu a zaben da ke tafe.

Ko a ranar Lahadi sai da gwamnonin APC suka yi taro da shugaban jam’iyyar na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, inda suka bukaci Shugaba Buhari ya bi umarnin Kotun Kolin.

Ba a haka a kasashen da suka ci gaba —Tinubu

A lokacin da kotun ta ba da umarnin wucin gadi na ci gaba da amfani da tsoffin kudin, Tinubu ya bayyana farin cikinsa, tare da cewa Najeriya ta kama hanyar fadawa cikin rudani da rashin tabbas ta bangaren tattalin arzikin da kuma siyasa sakamakon irin matakan da CBN ya dauka.

Tinubu ya ce kasashen da suka ci gaba kan bayar da wa’adin watanni 12 domin sauya kudin, yayin da ya yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su sake zama domin sake fasalin aikin ta yadda babu wani dan Najeriya da zai koka.

Shi ma Asusun Ba da Lamuni na Duniya IMF ya bukaci kara wa’adi ga jama’a domin ba su isasshen lokacin sauya kudaden nasu, yayin da yake cewa lokacin da CBN ya dauka ya yi kadan.

Matashiya

Tun da farko a ranar 31 ga watan Janairu CBN ya ce za a daina amfani da tsoffin takardun kudin naira 200, 500 da 1000.

Amma bayan korafe-korafe da aka yi ta yi, bankin ya kara kwanaki goma bayan sahalewar Shugaba Muhammadu Buhari.

Gabanin shigar da karar a kotu, gwamnonin jam’iyyar APC sun kai wa shugaba Buhari ziyara a fadarsa, inda suka nemi a kara wa’adin.

Ko da yake, ba su samu biyan bukata ba, amma Shugaban Kasar ya ce za a shawo kan matsalar karancin kudaden cikin kwanaki bakwai.

A halin da ake ciki, kotun ta ba bankuna da sauran cibiyoyin hada-hadar kudade a kasar umarni da su ci gaba da amfani da tsoffin kudaden har sai kotun ta yanke hukunci a zaman da za ta yi a ranar 15 ga watan Fabrairu.

Tun a watan Nuwambar bara, CBN ya soma fitar da sabbin kudaden da aka sauya wa fasali, sai dai karancin su ya jefa al’ummar kasar cikin halin ka-ka-ni-ka-yi.

’Yan Najeriya sun yi farin ciki

’Yan Najeriya sun jinjina wa Kotun Kolin saboda hukuncin da ta yanke na tilasta wa CBN yin watsi da wa’adin ranar 10 ga watan nan na dakatar da amfani da tsoffin kudaden da aka sauya wadanda karancinsu ya haifar da matsaloli baki daya.

Jama’ar kasar daga sassa daban-daban ciki har da talakawa da shugabanni da kuma malaman addinai sun bayyana korafinsu kan yadda aka samu matsala wajen sauyin, yayin da bankuna suka gaza samar da sabbin kudaden da ake bukata.

Wannan matsala ta sa aka fara samun bore a wasu biranen kasar da kuma kai hari a wasu bankuna, abin da ya kai ga rasa rai a birnin Abeokuta na Jihar Ogun.

Ko a birnin Ibadan, sai da ‘yan sanda suka tarwatsa gungun matasan da suka yi zanga-zanga domin nuna bacin ransu da karancin sabbin kudaden a bankuna, yayin da jama’a ke tururuwa domin neman su a bankuna.