Bayan karin albashi: Shin ƙungiyar ƙwadago za ta janye yajin aiki?
NLC ta ce duk da cewa alkawuran da gwamnati ta yi da kuma matsayar da suka cim-ma, har yanzu ba ta yanke shawara ba game da makomar yajin aikin da suka shirya shiga
A yau ne Ƙungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) za ta yanke shawara kan shirinta na fara yajin aikin sai abin da hali ya yi kan cire tallafin mai.
Ƙungiyar NLC, wadda ke shirin shiga yakin aiki domin neman karin albashin ma’aikata da sauran matakan rage raɗaɗin cire tallafin ta ce za ta yi zama da sauran rassanta ne bayan taron gaggawa da ta yi da Gwamnatin Tarayya ranar Lahadi.
- NAJERIYA A YAU: ‘Bai kamata ƙarin albashi ya tsaya a wata shida ba’
- Tinubu ya mayar da karin albashin da za a yi wa ma’aikata N35,000
Gwamnatin ta kira zaman ne jim kaɗan bayan Shugaba Tinubu ya sanar da ƙarin albashin N25,000 ga ƙananan ma’aikata a matsayin matakin wucin gadi na tsawon wata shida.
Gabanin zaman Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Femi Gbajabiamila, ya bayyana cewa duk ma’aikatan Gwamnatin Tarayya ne za a yi wa ƙarin albashin.
Gwamnatin ta kira zaman ne da nufin ganin da ƙungiyar ƙwadagon ta jingine shirinta na fara yajin aikin daga ranar Talata.
Abubuwan da aka cim-ma
A yayin zaman ne gwamnatin ta sanar cewa za ta yi wadannan abubuwan:
- Daga karin albashin da aka yi wa ma’aikata zuwa N35,000 na tsawon wata shida.
- Biyan iyalai miliyan 15 masu ƙaramin N25,000 a duk wata daga Oktoba zuwa Disamba don rage musu radadin cire tallafin mai.
- Ba da tallafi ga ƙananan masana’antu
- Dakatar da karbar harajin VAT a kan man dizel na tsawon wata shida
- Gaggauta samar da manyan motocin daukar fasinja masu amfani da iskar gas domin rage tsadar sufuri da tsabar fetur ya haifar.
A yayin zaman gwamnati ta jaddada bukatar ma’aikata su kasance a wuraren aikinsu, wanda ta ce sai da hakan al’amura za su tafi daidai.
Ta kuma bayyana fata cewa matakan da aka dauka da matsayar da aka cim-ma a zaman za su sa ƙungiyar ƙwadagon ta dakatar da shiga yajin aikin.
Sai mun tattauna —NLC
Bayan zaman ne Shugaba NLC, Joe Ajaero ya ce, duk da cewa an yi zaman da gwamnati kungiyar ba za ta yanke hukunci kan makomar yajin aikin da ta shirya shiga ba ita kaɗai.
Don haka sai ta tattauna da sauran kungiyoyin da ke ƙarƙashinta.
Tuni dai ƙungiyoyin ma’aikata da dama suka sanar da shirinsu na tsunduma yajin aikin da nufin ganin komai ya tsaya cak, sai gwamnati ta biya bukatunsu.
Ɓangarorin da suka nuna shirinsu na yajin aikin sun hada da fanni lafiya, ilimi, man fetur, sufuri da sauransu.
Fatan gwamnati
A yayin zaman gwamnati ta jaddada bukatar ma’aikata su kasance a wuraren aikinsu, wanda sai da hakan al’amura za su tafi daidai.
Gwamnatin ta bayyana fata cewa matakan da aka dauka za su sa ƙungiyar ƙwadagon ta dakatar da shiga yajin aikin.
Ministan Yada Labarai Mohammed Idris, ya ce an yi karin N10,000 a kan N25,000 da Shugaba Tinubu ya sanar a lokacin jawabinsa na cikar Najeriya shekara 63 da samun ’yanci ne a bisa bukatar kungiyoyin.
Ya ce gwamnati na fada kungiyoyin za su amince da bukatar da dakatar da yajin aikin, saboda sai suna aiki ne za a iya tattauna batutuwan da suka gabatar yadda ya kamata.
A nasa banganren, Gbajabiamila ya ce suna da kwarin gwiwa cewa abubuwan da aka tattauna da kuma matsayar da aka cim-ma za su amfani ma’aikata.