Yau Lahadi za mu sanya hannu a yarjejeniya da Iran — Trump

Trump ya kuma ce nan take bayan ƙulla yarjejeniyar, za a buɗe Mashigar ruwa ta Hormuz ga dukkan jiragen ruwa.

Yau Lahadi za mu sanya hannu a yarjejeniya da Iran — Trump

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa ana sa ran rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Amurka da Iran a yau Lahadi, domin kawo ƙarshen yaƙin da ya ɗauki watanni ana gwabzawa a Gabas ta Tsakiya.

Trump ya kuma ce nan take bayan ƙulla yarjejeniyar, za a buɗe Mashigar ruwa ta Hormuz ga dukkan jiragen ruwa, bayan watanni da rikicin ya jefa harkokin sufuri da kasuwancin mai cikin ruɗani.

Kalaman na Trump sun zo ne yayin da Iran, masu shiga tsakani da kuma ƙasashen da abin ya shafa ke nuna ƙwarin gwiwar cewa tattaunawar da aka shafe makonni ana yi tana gab da haifar da ɗa mai ido.

Firaministan Pakistan, Shehbaz Sharif, wanda ƙasarsa ke taka muhimmiyar rawa wajen sasanta rikicin, ya ce a wannan karon, cimma yarjejeniyar ta fi kusa da kowane lokaci aka samu a baya.

A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, Sharif ya ce ana sa ran kammala yarjejeniyar cikin sa’o’i 24 masu zuwa, sannan a rattaba hannu a kanta.

Sai dai kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran, Esmaeil Baqaei, ya ce har yanzu ba a tantance ranar sanya hannu kan yarjejeniyar ba, ko da yake ya amince cewa hakan na iya faruwa cikin ‘yan kwanaki masu zuwa.

Makomar Mashigar Hormuz

Daya daga cikin manyan batutuwan da suka jawo saɓani a tattaunawar shi ne makomar Mashigar Hormuz, wadda ke zama muhimmiyar hanyar jigilar mai da iskar gas ta duniya.

Tun bayan da Iran ta sanya takunkumi a kan zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar, ta buƙaci jiragen ruwa su nemi izininta kafin wucewa tare da kafa wata hukuma ta musamman domin kula da harkokin mashigar.

Sai dai Trump ya ce bayan rattaba hannu kan yarjejeniyar, mashigar za ta kasance a buɗe ga kowa ba tare da wani cikas ba.

A gefe guda kuma, Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi, ya jaddada cewa ƙasarsa za ta ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen tafiyar da harkokin mashigar, yana mai bayyana ta a matsayin ɗaya daga cikin manyan hanyoyin kare muradun Iran.

Batun shirin nukiliyar Iran

Har ila yau, makomar shirin nukiliyar Iran na daga cikin manyan batutuwan da ke ci gaba da janyo muhawara tsakanin ɓangarorin biyu.

Iran ta dage cewa tana aiwatar da shirinta na nukiliya kaɗai ne saboda zaman lafiya, kuma tana da haƙƙin ci gaba da tace sinadarin uranium.

Amma Amurka da Isra’ila na zargin cewa Tehran na neman ƙera makamin nukiliya.

Trump ya ce idan aka cimma yarjejeniya, za a tattara ragowar sinadaran nukiliyar da ake taƙaddama a kansu domin lalata su ko dai a cikin Iran ko kuma a Amurka.

Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya ce Trump ya tabbatar masa cewa duk wata yarjejeniya da za a cimma dole ne ta haɗa da karɓe sinadarin uranium mai matuƙar ƙarfi daga hannun Iran.

Duk da haka, wasu mazauna Tehran sun nuna shakku kan yiwuwar cimma yarjejeniyar cikin gaggawa, inda suke zargin cewa har yanzu ba su da cikakken yaƙinin cewa tattaunawar za ta kai ga sakamakon da ake fata.