Yau Madrid za ta hadu da Man City gobe kuma Manchester United da FC Barcelona
A yau Juma’a 24 ga watan Yuli ne kulob din Real Madrid da ke Sifen zai kece raini da na Manchester City da ke Ingila a wasannin share fage don tunkarar kakar wasa mai zuwa da Amurka ta shirya da ake wa lakabi da International Champions Cup. A gobe Asabar ne kuma ake sa ran […]
A yau Juma’a 24 ga watan Yuli ne kulob din Real Madrid da ke Sifen zai kece raini da na Manchester City da ke Ingila a wasannin share fage don tunkarar kakar wasa mai zuwa da Amurka ta shirya da ake wa lakabi da International Champions Cup. A gobe Asabar ne kuma ake sa ran Manchester United za ta hadu da kulob din FC Barcelona da ke Sifen duk a gasar.
Gasa ce da Amurka take shiryawa a duk shekara kafin a fara kakar wasa. Kuma kimanin manyan kungiyoyin kwallon kafa daga sassan duniya ne kasar ke gayyatarsu don fafatawa a Amurka.
A bana kasar ta gayyaci kungiyoyin kwallon kafa 13 ne da suka hada da Real Madrid da FC Barcelona daga Sifen, yayin da ta gayyaci kulob din Roma da AC Milan da AC Fiorentina da kuma Inter Milan daga Italiya. Sai Manchester United da Manchester City da Chelsea dukkaninsu daga Ingila sai kulob din PSG daga Faransa. Haka kuma akwai New York Red Bulls da Los Angels Galady daga Amurka da kuma kulob din SL Benfica daga Fotugal.
Duk kungiyar da ta fi samun yawan maki a gasar ce za ta zama zakara.