Yau Majalisar za ta ci gaba da aiki kan Dokar Haraji
Masu ruwa da tsaki sun kasa sun tsare domin ganin yadda za ta kaya a Majalisar Dokoki ta Kasa kan dokar mai cike da rudani
A Talatar nan Majalisar Dokoki ta kasa ta ci gaba zama don hanzarta kammala aiki kan ƙudirin sabuwar dokar haraji mai cike da ruɗani da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gabatar mata.
Bayan zaman farko a ranar 14 da watan nan na Janairu, ta dage zama zuwa ranar 28 domin kwamitoci su kammala aikin tantance kasafin 2025, amma daga bisani ta sake dage zuwa 4 ga Fabrairu domin kwamitocinta su gama sauraron kare kasafin hukumomin gwamnati.
Kafin tafiyar majalisar hutu, an tayar da jijiyoyin a Najeriya kan wasu dokoki hudu na haraji da Shugaba Tinubu ya gabatar wa Majalisar a ranar 13 ga Oktoban 2024.
Gwamnoni da sauran masu ruwa da tsaki na yankin Arewa na zargin dokokoin da nufin danniya da neman talauta yankin, inda suka bukaci a soke dokar.
- Yau Majalisar za ta ci gaba da aiki kan Dokar Haraji
- Kotu ta yanke wa mutum 5 hukuncin rataya a Kano
Amma daga bisani bayan zaman da kungiyar gwamnoni ta kasa (NGF) da Kwamitin Shugaban Kasa kan dokar harajin, aka samu daidaito inda masu adawa da ita suka mayar da wukakensu cikin kube.
Daga cikin matsayar da suka cimma akwai rabon kashi 30% na kudaden harajin sayen kayayyaki (VAT) ga jihohin da aka sayi kayan, maimakon 60% da Tinubu ya nema.
Sun kuma amince da raba 50% na VAT daidai a tsakanin duk jihohi, ragowar 20% kuma gwargwadon yawan al’ummar kowace jiha domin tabbatar da adalci.
Bayan nan ne Gwamna Abdullahi Sule na Jihar Nasarawa ya ce za su nemi goyon bayan ’yan majalisar dokoki ta kasa daga jihohinsu domin ganin dokar ta samu shiga.
Wakilinmu ya ruwaito cewa masu ruwa da tsaki, ciki har da wasu gwamnoni sun kasa sun tsare domin ganin yadda za ta kaya a Majalisar Dokoki ta Kasa kan lamarin dokar mai cike da rudani.